7 GA JANAIRU, 2021
FIJI
Mahaukaciyar Guguwar Yasa Mai Mataki Biyar Ta Yi Barna a Fiji
Inda ya faru
Fiji
Bala’i
A ranar 17 ga Disamba, 2020, wata guguwa mai tsanani da ake kira Yasa ta yi barna a tsibiri na biyu da ya fi girma a Fiji, wato tsibirin Vanua Levu
Yasa ce guguwa ta biyu mafi girma da ta taba aukuwa a Fiji. Mai yiwuwa guduwar iskar ya kai kilomita 260 a cikin awa daya (ko mil 161 a cikin awa daya)
Akalla ikilisiyoyi da rukunoni 30 ne ke wannan yankin
Yadda ya shafi ’yan’uwanmu
Babu dan’uwa ko ’yar’uwa da ta ji rauni
Rahotannin da aka fara samuwa sun nuna cewa iyalai 20 sun gudu sun bar gidajensu
Guguwar ta lalata gonaki da yawa, kuma musamman daga gonakin ne masu shela 430 da suke zama a yankin suke samun abinci
Abubuwan da aka yi hasararsu
Gidaje 10 sun rushe
Gidaje 25 sun lalace
Majami’ar Mulki guda 1 ya dan lalace
Agaji
Reshen ofishinmu na Fiji ya kafa Kwamitin Agaji guda uku. Wadannan kwamitin agajin sun tanadar abubuwa kamar ruwan sha mai kyau da riguna da abinci da tampolin wa masu shelar da bala’in ya shafa. Kari ga haka, kwamitin sun samar ma wadanda suka rasa gidajensu matsuguna
Wakilai daga ofishinmu na Fiji tare da masu kula da da’ira da ke yankin suna kai ziyarar karfafa ga ’yan’uwan da bala’in ya shafa
Duka ’yan’uwa da suke ba da agaji da kuma kai ziyarar karfafa suna bin ka’idodin kāriya da aka kafa don cutar koronabairas
Ko da yake ’yan’uwanmu sun yi hasara saboda wannan mummunar guguwar, sun yarda da kalmomin da ke Zabura 46:1 cewa: “Allah shi ne wurin buyanmu.”