Koma ka ga abin da ke ciki

26 GA MAYU, 2017
RASHA

An Kama Wani Mashaidi Dan Denmark a Rasha Sa’ad da ’Yan Sanda Suka Kai Hari a Wajen Ibada

An Kama Wani Mashaidi Dan Denmark a Rasha Sa’ad da ’Yan Sanda Suka Kai Hari a Wajen Ibada

NEW YORK​—⁠An kama wani dan Denmark tare da wasu ’yan Rasha a sakamakon hukuncin da Babbar Kotun Rasha ta tsayar game da Shaidun Jehobah a ranar 20 ga Afrilu 2017. Hakan ya faru ne a yammancin 25 ga Mayu, 2017 lokacin da suke taronsu na ibada cikin lumana sai ’yan Sanda suka kai masu hari.

Dennis Christensen

Akalla ’yan sanda 15 ne suke dauke da makamai tare da wakilan Federal Security Service (FSB) da suka kai hari wajen taron ibadar Shaidun Jehobah da suke yi cikin lumana a birnin Oryol (wanda aka saba kira Orel), ga hoto a bisa. ’Yan sanda sun kwace takardun shaidar zaman kasa daga duk wanda ya halarci taron kuma sun kwace duk wayoyin tarho dinsu. FSB sun kuma kulle wani dan Denmark Denis Christensen, daya daga cikin Shaidun Jehobah. Ba da dadewa ba sai ’yan sanda suka yi binciken gidaje huɗu na Shaidun Jehobah da ke cikin birnin.

Bayan da ya kwana a hanun FSB, sai Kotun Oryol ta amince da karar da FSB suka kai kuma Kotun ta ce a tsare Mallam Christensen a kurkuku, nan zai yi jira har sai lokacin da FSB za su gama duk wani binciken da za su yi. Mallam Christensen ne na farko cikin bakin da ke kasar da Babban Kotun Rasha ta hukunta tare da sauran Shaidun Jehobah bayan matakin da Kotun ta dauka. In dai an ba shi laifi, Mallam Christensen zai dade a kurkuku.

Wannan mummunar hari na 40 kenan da ake kai wa Shaidun Jehobah wanda ’yan sanda da wasu ke ta yi bayan da Babban Kotu ta sharanta su da halin tsattsauran ra’ayi, ta kuma ƙwace Ofishinsu na Rasha tare da wurare 395 a kasar da suke ibadarsu.

’Yan ta’adda sun kone wani gida inda ake taron ibada.

Bayan dan lokaci a ranar 20 ga Afrilu a lokacin da Babban Kotun ta yanke shari’a, sai wasu maza a St. Petersburg suka lalatar da wurin ibadar Shaidun Jehobah mafi girma a Rasha, har ma da razanar da ’yan Ibada. Sun kuma kai hari a wasu wuraren ibada da gidajen Shaidun Jehobah a Kaliningrad, Moscow, Penza, Rostov, St. Petersburg da Sverdlovsk da Voronezh da kuma Krasnoyarsk. A wani loƙaci, ranar 24 ga Mayu, 2017, a ciki garin Zheshart a Komi Republic, an yi mummunar barna a wani gida wanda shaidun Jehobah ke halartar taro. Ban da harin da ‘yan sanda suke kai wa da kuma barnar da ake yi wa Shaidun Jehobah, suna kuma fuskantar barazana a makaranta da wurin aiki, ana ma koransu a wurin aiki.

David A. Semonian, kakakin Shaidun Jehobah a hedkwatarsu, ya ce: Shaidun Jehobah a fadin duniya suna damuwa sosai game da ’yan’uwanmu a Rasha. Wannan mawuyacin halin sakamakon shari’ar rashin adalcin da Babban Kotun Rasha ta yanke akan mu ne. Mun yi afil din shari’ar da suka yanke a ranar 19 ga Mayu, 2017. Wannan zai sake ba Rasha zarafi don su kawo karshe ga wannan halin cin mutunci da rashin adalci da ake yi wa Shaidun Jehobah. Har ila muna shirin kai wata kara saboda halin rashin adalcin rike dan’uwanmu Dennis Christensen a kurkuku.

Inda Aka Sami Labarin

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000