Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
Mece ce amsarka?
-
E.
-
A’a.
-
Wataƙila.
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
“Allah . . . zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4, Littafi Mai Tsarki.
ABIN DA ZA KA IYA MORA SABODA ALKAWARIN NAN
Za ka kasance da tabbaci cewa ba Allah ne sanadin matsalolinmu ba.—Yaƙub 1:13.
Za ka sami kwanciyar hankali saboda sanin cewa Allah ya damu da mu sa’ad da muke shan wahala.—Zakariya 2:8.
Za mu kasance da bege cewa dukan wahala za ta ƙare.—Zabura 37:9-11.
ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?
Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai biyu:
-
Allah ya tsani wahala da rashin adalci. Ka yi la’akari da yadda Jehobah Allah ya ji sa’ad da aka tsananta wa mutanensa a zamanin dā. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya damu saboda “waɗanda suka tsananta masu da wulaƙanci.”—Alƙalawa 2:18.
Allah ya tsani waɗanda suke wulaƙanta mutane. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana ƙyamar “masu-zub da jinin mara-laifi.”—Misalai 6:16, 17.
-
Allah ya damu da kowannenmu. Hakika, kowane mutum yana ‘sane da nasa annoba da nasa baƙin ciki,’ kuma Jehobah ma yana sane da hakan!—2 Labarbaru 6:29, 30.
Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa wajen kawo ƙarshen matsalolin da kowannenmu yake fuskanta. (Matta 6:9, 10) A yanzu hakan ma, yana ƙarfafa dukan waɗanda suke biɗar sa da gaske.—Ayyukan Manzanni 17:27; 2 Korintiyawa 1:3, 4.
KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR
Me ya sa Allah ya kyale shan wahala?
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a ROMAWA 5:12 da kuma 2 BITRUS 3:9.