Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Halittu Suke Koya Mana?

Mene ne Halittu Suke Koya Mana?

Mene ne Halittu Suke Koya Mana?

Amma dai tambayi dabbobin daji, za su koyar da kai, tsuntsayen sararin sama za su koya maka. Yi magana da kasa, za ta koyar da kai, kifaye na cikin teku ma za su sanar da kai.​—AYUBA 12:7, 8.

’YAN KIMIYYA da injiniyoyi sun koyi abubuwa da yawa daga halittu. Suna kwaikwayon abubuwan da suka gani a dabbobi da tsire-tsire. Suna yin hakan ne don su inganta abubuwan da suka yi ko kuma ma su yi wasu sabbi. Ka yi la’akari da wadannan halittun kuma ka tambayi kanka, ‘Wane ne ya halicce su? Wa ya kamata a yaba wa?’

Kwaikwayon Hannayen Kifin da Ake Kira Whale

Makeran jirgin sama za su iya koyan abubuwa da yawa daga kifin da ake kira humpback Whale. Nauyin babba daga cikinsu yakan kai tan 30 kamar nauyin babbar mota da aka cika masa kaya. Jikinsa yana da kauri kuma yana da manyan hannaye da suke kama da fuka-fukai. Wannan babban kifin yana da tsayin kafa 40 kuma yana tafiya a saukake a cikin ruwa. Alal misali, Idan kifin ya ga kananan kifayen da yake so ya ci, yakan koma karkashinsu kuma ya dinga zagayawa yana fitar da wani irin kumfa. Kumfa-kumfan sukan zama kamar raga da ke tara kifayen wurin daya, sa’an nan babban kifin ya zo ya hadiye su.

‘Yan kimiyya ba su fahimci yadda wannan babban kifin yake iya jujjuyawa da wuri haka ba. Daga baya sun gano cewa hannayensa ne suke taimaka masa ya yi hakan. Gaban hannayensa bai da laushi kamar na jiragen sama. Maimakon haka, kamar kunya-kunya yake.

Kunya-kunyan nan sukan sa ya yi wa kifin sauki ya dinga haurawa a cikin ruwa. Wata mujallar mai suna Natural History ta bayyana cewa kunyan-kunyan ne suke sa ruwa ya dinga gudu a hanyar da za ta taimaka wa kafin ya yi saurin haurawa a cikin ruwa. Da a ce babu kunya-kunyan nan a hannayen kifin, da hakan ba zai yiwu ba.

Ta yaya sanin abubuwan nan zai taimaka? Idan aka yi fuka-fukan jirgin sama kamar hannayen kifin humpback whale, za su zama da saukin amfani, da inganci kuma ba za su yi saurin lalacewa ba. Wani masani mai suna John Long ya ce da alama cewa nan ba da dadewa ba, “duka jiragen sama za su zama masu hannaye irin na kifin humpback whale.”

Kwaikwayon Fuka-Fukan Tsuntsun da Ake Kira Seagull

Masu kera jiragen sama sun riga sun yi kwaikwayon fuka-fukan tsuntsaye. Amma yanzu sun kyautata yadda suke hakan sosai. Wata mujalla mai suna New Scientist ta ce, “masu bincike a Jami’ar Florida sun yi kokarin sun kera jiragen sama da za su rika tashiwa kamar tsuntsun Seagull. Sun yi jirgi marar matuki da ake kira drone da ke iya tashi da kuma gudu da wuri kuma yake iya tsayawa a wuri daya a sama.”

Tsuntsayen Seagull sun iya firewa sosai domin suna iya karkata fuka-fukansu a kafada da kuma gwiwar hannunsu. Mujallar ta kuma bayyana cewa “karamin jirgin nan da aka yi yana da kufa-fukan da suke aiki kamar tsuntsun Seagull.” Fuka-fukan nan suna taimaka wa karamin jirgin ya iya tsayawa a iska kuma ya yi gudu tsakanin dogayen gidaje. Jami’an tsaro za su so su yi amfani da irin wadannan jirage wajen bincika duk inda aka boye makamai a manyan birane.

Kwaikwayon Kadangaren da Ake Kira Gecko

Dabbobin da suke tafiya a kasa ma za su iya koya mana abubuwa da yawa. Alal misali, karamin kadangaren nan mai suna gecko ya iya hawan bango sosai har ma ya manne a kan silin ba tare da fadowa ba. Me ke taimaka wa kadangaren ya yi hakan?

Suma-suma da ke jikin kafaffun gecko ne suke taimaka masa ya iya manne wa abubuwa masu santsi kamar gilashi. gecko bai da wani gam a kafaffunsa. Kwayoyin halitta da ke kafaffun geckon ne suke sa shi ya manne wa abubuwa. Ba za mu iya manne wa bango ko silin ba. Amma kadangaren nan zai iya yin hakan domin suma-suman da ke tafin kafaffunsa.

Wane amfani za a iya samu daga wannan binciken? Za a iya amfani da shi wajen kera abin da zai rike abubuwa biyu tare maimakon irin abu mai suma-suma da ake rike takalmi da shi mai suna Velcro. * A mujallar nan The Economist, wani mai bincike ya ce za a iya yin amfani da abu mai irin tsarin kafar gecko wajen rufe raunuka a wuraren da ba za a iya amfani da sauran kayan rufe rauni ba.

Wa Ya Kamata A Yaba Masa don Wadannan Halittun?

Ma’aikatar Binciken Sararin Samaniya, wato NASA ta kera wata na’ura da take tafiya kamar kunama. A kasar Finland kuma, wasu injiniyoyi sun kera wata katafilla da take masar da kayayyaki kamar yadda babban kwaro yake yi. Wasu masu bincike sun tsara wasu kayan sakawa su rika canjawa kamar yadda wani shuka mai suna pinecones yakan budu da kuma rufu bisa ga yanayi. Wani kamfanin mota sun kera wata mota mai inganci da iska ba ya jan ta sosai bisa ga tsarin jikin wani kifi mai suna boxfish. Wasu masana suna nan suna binciken bayan wani irin dodon kodi mai suna abalone kuma manufarsu ita ce su kera wani kayan kāre jiki kamar sa.

Ta wurin binciken halittu, masana sun sami hikimar yin abubuwa da yawa kuma hakan ya sa sun yi wata na’ura da ke dauke da wadannan bayanan. ’Yan kimiyya sukan bincike wannan na’ura da ke dauke da bayanai game da halittu don su san yadda za su warware matsalolin da suke fuskanta a abubuwan da suka kera. Masana sun kira wannan bayanan biological patent. Mutum ko kuma kamfanin da yake rike da sabbin bayanai da aka kawo shi ne ake kira patent holder. Da suke tattauna game da bayanan nan, mujallar nan The Economist ta ce: “Tun da sun kira bayanan biological patent, hakan ya nuna cewa ainihin halittu ne ke rike da bayanan.”

Me ya sa halittu suke dauke da bayanan nan masu kayatarwa? Masana da yawa suna ganin cewa hakan ya faru ne domin miliyoyin shekarun da halittu suka yi suna canja da kuma gyara kansu. Wasu masana kuma suna da wani ra’ayi dabam. Wani masani mai suna Michael Behe ya rubuta a jaridar The New York Times na 2005 cewa: “Da yake muna ganin tabbacin abubuwa, ba ma bukatar wani ya sake tabbatar mana. Hakazalika, da yake ana koyan yadda za a kera abubuwa daga halittu, hakan ya nuna cewa akwai wanda ya yi su.”

Babu shakka, muna bukatar mu yaba ma wanda ya yi fuka-fukan jirgin sama da suke aiki da kyau. Haka ma ya kamata a yaba ma wadanda suka yi bandeji da kayan sakawa masu kyau da kuma motoci. Akan hukunta duk wani da ya yi koyi da wani abu da wani ya kera ba tare da yaba masa ba.

Masana masu ilimi sun iya magance abubuwa da yawa ta bayanan da suka samu daga halittu. Shin kuna ganin ya dace a ce wadannan abubuwan sun faru ne daga juyin halitta ba tare da wani mai hikima sosai da ya halicce su ba? Idan sai mai ilimi ne zai iya kwaikwayon abu, shin wanda ya halicci ainihin abin bai fi shi ilimi ba ne? A cikin su biyu, wa ya kamata a yaba masa, wanda ya halicci abu ko kuma wanda ya yi kwaikwayonsa?

Me Hakan Ya Koya Mana?

Bayan da mutane da yawa suka bincika hikimar da ke tattare da halittu, sun yarda da abin da wani marubucin zabura ya ce: “Ya Yahweh, ina misalin yawan ayyukanka, cikin hikima ka yi su duka! Duniya cike take da halittunka.” (Zabura 104:24) Wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Bulus ma ya yarda da hakan. Ya ce: ‘Halin Allahntaka na Allah da kuma ikonsa na har abada ba abubuwan da ake iya gani da ido ba ne. Amma tun halittar duniya an bayyana wadannan abubuwan a fili, ana kuma iya gane su bisa ga abubuwan da aka halitta.’​—Romawa 1:​19, 20.

Har ila akwai mutane da yawa da suke daraja Littafi Mai Tsarki kuma suka yi imani da Allah, amma suna cewa Allah ya yi amfani da juyin halitta ne wajen halittar abubuwa masu kyau da muke gani. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan?

[Ƙarin bayani]

^ sakin layi na 15 Velcro wani abu ne mai suma-suma da ake amfani da shi don a manne abubuwa da aka kirkiro shi ta wajen yin koyi da kwayar wata shuka mai suna burdock.

[Bayani]

Me ya sa halittu suke da abubuwa da yawa da za mu iya koya daga gare su?

[Bayani]

Wane ne tushen bayanan da ake samu daga halittu?

[Akwati/​Hotuna]

Idan sai mai ilimi ne zai iya kwaikwayon abu, shin wanda ya halicci ainihin abin bai fi shi ilimi ba ne?

An kwaikwayi fuka-fukan tsuntsun seagull wajen kera jirgin nan

Tafin kadangare mai suna gecko ba ya datti kuma ba a ganin sawun kafarsa, yana masa sauki ya manne a jikin kowanne abu kuma ya bar abin amma ban da wani irin abu da ake kira Teflon. Masana suna kokari wajen yin koyi da su

An bi tsarin jikin kifin boxfish wajen kera wata ingantacciyar mota

[Wuraren da Aka Ɗauko]

Airplane: Kristen Bartlett/​University of Florida; gecko foot: Breck P. Kent; box fish and car: Mercedes-Benz USA

[Akwati/​Hotuna]

MATAFIYA MASU HIKIMA SOSAI

Dabbobi da dabam suna da ‘hikimar’ yin tafiye-tafiye ba tare da sun bata ba. (Karin Magana 30:​24, 25) Bari mu bincika misali guda biyu.

Yadda Kyashi Suke Yin Tafiye-Tafiye Yaya kyashi suke sanin hanyar dawowa bayan sun yi tafiya mai nisa suna neman abinci? ’Yan kimiyya a Ingila sun gano cewa kyashi sukan bar wani irin wari a sawunsu kuma sukan saka maki a hanyar da suke bi don su san hanyar dawowa gida. Alal misali, akwai wani irin kyashi da suke barin maki a hanyar da suke bi kuma sukan rarraba hanyar kashi biyu. Wata mujalla mai suna New Scientist ta bayyana cewa kyashin nan sun san gefen da suke saka makin. Yadda hakan yake taimaka musu abin ban sha’awa ne. Domin idan suka kai inda hanyar ta rabu kashi biyu sukan san hanya mafi sauki da za su bi don su isa gida. Wannan tsarin ne yake sa ya yi wa kyashi sauki su dinga yin tafiye-tafiye ba tare da sun bata ba.

Abin da Ke Taimaka wa Tsuntsaye Su San Hanyar da Za Su Bi Idan tsuntsaye suka tashi kaura, sukan yi tafiya mai nisa a yanayi dabam-dabam amma ba sa batawa. Me yake taimaka musu su yi hakan? Masu bincike sun gano cewa tsuntsaye suna amfani da karfin maganadisun duniya. Amma wata mujalla ta bayyana cewa karfin maganadisun duniya yakan canja kuma ba a kullum yake yin nuni ga wuri daya ba. Ta yaya tsuntsayen suke sanin hanyar da za su bi? Idan yamma ta yi, tsuntsayen sukan yi amfani da inda rana take don su san hanyar da za su bi. Ko da yake rana ba ta tsayawa a wuri daya a duk shekara, tsuntsayen suna iya sanin lokacin da ake ciki. Tsuntsayen sukan harhada wadannan bayanan don su san hanyar da za su bi.

Wa ya koya wa kyashi hikimar sanin hanyar da za su bi? Wa ya koya wa tsuntsaye yadda za su san hanyar da za su bi? Juyin halitta ne, marar tsari? Ko kuma wani Mahalicci mai hikima ne ya yi hakan?

[Inda Aka Ɗauko]

© E.J.H. Robinson 2004