ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
Caca
Wasu mutane suna ganin yin caca wata hanya ce mai kyau ta samun kudi, wasu kuma suna ganin yana cike da hadari.
Shin yin caca laifi ne?
ABIN DA MUTANE SUKE CEWA
Mutane da yawa suna ganin cewa yin caca ba laifi ba ne muddin doka ba ta hana ba. Gwamnati ma takan shirya wasu irin caca da doka ta amince da su don ta samo kudin da za a taimaka wa jama’a da shi.
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
Ba a ambaci caca a Littafi Mai Tsarki ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba da wasu ka’idodi da suka nuna ra’ayin Allah game da yin caca.
A caca, kudin da wasu suka yi hasarar sa ne mutum yake ci, kuma hakan ya saba wa gargadin da ke Littafi Mai Tsarki cewa mu yi “nesa da kowane irin kwadayi.” (Luka 12:15) Kwadayi ko hadama ce take sa mutum ya yi caca. Kamfanonin caca sukan yi talle cewa mutum zai ci dunbin kudi. Sun san cewa mutane kalilan ne kawai za su iya cin kudin amma ba sa fadin hakan don sun san cewa son yin arziki zai sa mutane su sa kudi da yawa a cacar. Caca takan zuga mutum ya so samun kudi cikin sauki maimakon ta taimaka masa ya guji yin hadama.
Son kai ne yake sa mutane su so yin caca domin suna son wasu su yi hasarar kudinsu, don su su ci. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce, “kada ka yi wa kanka kadai abu mai kyau, amma ka yi wa dan’uwanka kuma.” (1 Korintiyawa 10:24) Wata Dokar da Allah ya bayar ta ce: “Ba za ka yi kwadayin . . . wani abin da makwabcinka yake da shi ba.” (Fitowa 20:17) Manufar mai yin caca ita ce, wasu su yi hasarar kudinsu domin shi ya samu riba.
Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa bai kamata mu dauki sa’a a matsayin wani irin Allah da ke sa mu sami albarka ba. A zamanin Isra’ilawa, akwai wadanda suka nuna rashin bangaskiya kuma suka soma “shirya tebur domin gunkin nan Wadata (Sa’a, Littafi Mai Tsarki).” Shin Allah ya ji dadi da ya ga irin ibadar da suke yi wa allahn “Sa’a”? A’a, shi ya sa ya gaya musu cewa: “Kuka aikata mugunta a idona, kuka zaba ku yi abin da ban ji dadinsa ba.”—Ishaya 65:11, 12.
Ko da yake a wasu wurare, ana amfani da kudin da aka samo daga yin caca wajen biyan kudin makaranta da bunkasa tattalin arziki da dai sauransu, hakan ba ya nufin cewa yadda aka samo kudaden ya dace. Domin an samo su ne daga ayyukan da ke sa mutane su kasance masu hadama da son kai kuma su so samun abubuwa ba tare da sun yi aiki ba.
“Ba za ka yi kwadayin . . . wani abin da makwabcinka yake da shi ba.”—Fitowa 20:17.
Ta yaya yin caca zai iya shafan mai yin caca?
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
Littafi Mai Tsarki ya mana gargadi cewa “wadanda suke marmarin yin arziki sukan fādi cikin jarraba, cikin tarko na mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na banza, da na cutar wadanda sukan sha kansu, su jawo su zuwa ga lalacewa da halaka.” (1 Timoti 6:9) Hadama ko kuma kwadayi ne yake sa mutane yin caca. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce irin wannan ‘kwadayin’ yana cikin mugayen halayen da ya kamata mu guje musu.—Afisawa 5:3.
Yin caca yana sa mutum ya zama mai son kudi domin yana sa mutum ya ga cewa zai iya samun kudi cikin sauki. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce kaunar kudi “ita ce tushen kowace irin mugunta.” Son yin kudi zai iya shawo kan mutum kuma ya sa ya soma yawan damuwa har ya bata dangantakarsa da Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce wadanda suka kamu da jarabar son kudi sukan “jawo wa kansu bakin ciki iri-iri masu zafi.”—1 Timoti 6:10.
Hadama takan hana mutum gamsuwa da abin da yake da shi, har ma ya soma bakin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai son kudi, ba ya koshi da shi, mai son arziki ma, ba ya koshi da abin da yake samuwa.”—Mai-Wa’azi 5:10, Littafi Mai Tsarki.
Miliyoyin mutanen da suka shiga yin caca, hakan ya zama musu jaraba. Matsalar ta yi yawa sosai har an kimanta cewa akwai miliyoyin mutane da suka kamu da jarabar yin caca a Amirka kawai.
Wani karin magana ya ce: “Gādon dukiyar da aka samu da sauri a farko, ba shi da albarka a karshe.” (Karin Magana 20:21) Wadanda suke da jarabar yin caca sun shiga cikin bashi. Wasu ma cacar ta sa sun rasa aikinsu da aurensu har da abokansu. Bin gargadin da ke Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa mutum ya guji mummunar sakamakon da yin caca yake kawo wa.
“Wadanda suke marmarin yin arziki sukan fādi cikin jarraba, cikin tarko na mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na banza, da na cutar wadanda sukan sha kansu, su jawo su zuwa ga lalacewa da halaka.”—1 Timoti 6:9.