Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Allah Ya Yi Mana Alheri Sosai

Allah Ya Yi Mana Alheri Sosai

DA YAKE mahaifina mai suna Arthur yana tsoron Allah, ya so ya zama limamin cocin Methodist. Amma hakan bai yiwu ba saboda Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma nazari da shi kuma ya yi baftisma a shekara ta 1914. Kuma a wannan lokacin shekararsa 17 ne. A wannan lokacin ne aka soma Yaƙin Duniya na Ɗaya, don haka, aka ce ya shiga soja. Saboda ya ƙi yin yaƙi, sai aka tura shi kurkukun da ake kira Kingston Penitentiary da ke jihar Ontario a ƙasar Kanada. Bayan da aka saki mahaifina daga kurkuku, sai ya soma hidimar majagaba.

A shekara ta 1926, mahaifina Arthur Guest ya auri Hazel Wilkinson, wadda mahaifiyarta ta koyi gaskiya a shekara ta 1908. Sai suka haife ni a ranar 24 ga Afrilu shekara ta 1931 kuma ni ne na huɗu cikin yaran. Ba ma wasa da ibada a iyalinmu, kuma yadda mahaifina yake daraja Littafi Mai Tsarki ya sa mu ma muna yin hakan har yanzu, dukanmu muna yin wa’azi gida-gida.A. M. 20:20.

NA SOMA HIDIMAR MAJAGABA KUMA NA ƘI SHIGA SOJA, KAMAR YADDA BABANA YA YI

An hana Shaidun Jehobah yin aikinsu a ƙasar Kanada bayan shekara ɗaya da aka soma Yaƙin Duniya na Biyu a shekara ta 1939. Makarantu sun yi bukukuwa na kishin ƙasa da suka ƙunshi sara wa tuta da kuma yin waƙar taken ƙasa. Ana koran ni da ‘yar’uwata mai suna Dorothy daga aji a duk lokacin da ake yin bukukuwan nan. Wata rana malamarmu ta so ta disga ni, kuma ta kira ni matsoraci. Bayan an tashi daga makaranta ‘yan ajinmu suka soma zagi na har ma suka yi mini dūkan tsiya. Amma abin da suka yi ya sa na yi tsayin daka cewa wajibi ne in “yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”A. M. 5:29, Littafi Mai Tsarki.

A watan Yuli na shekara ta 1942 sa’ad da nake shekara 11 na yi baftisma a wani babban tankin ruwa a wurin da ake kiwon dabbobi. Na ji daɗin yin amfani da hutun makaranta don hidimar majagaba na ɗan lokaci. Akwai shekarar da na bi wasu ‘yan’uwa uku zuwa yankin da ba a yawan yin wa’azi a arewacin yankin Ontario don mu yi wa mutanen da ke sare bishiya a wajen wa’azi.

A ranar 1 ga Mayu a shekara ta 1949 na soma hidimar majagaba na kullum. Da yake ana gini a ofishin da ke Kanada, an gayyace ni na zo hidima a Bethel da ke Kanada a ranar 1 ga watan Disamba. Na yi aiki a wajen da ake buga littattafai kuma hakan ya sa na koyi yin amfani da injin buga littattafai. Makonni da yawa na yi aikin dare don muna buga wata warƙa da ta yi magana game da irin tsanantawar da ake yi wa Shaidun Jehobah a ƙasar Kanada.

Bayan haka, da nake aiki a Sashen Hidima, na tattauna da wasu majagaba da suka zo ziyara a Bethel da suke so su je hidima a yankin Quebec inda ake tsananta wa Shaidun Jehobah. Sunan ɗaya daga cikinsu shi ne Mary Zazula kuma ta fito ne daga Edmonton wani birnin da ke jihar Alberta. Iyayenta ‘yan cocin Orthodox sun kore ta da yayanta don sun ƙi su daina yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. A watan Yuni na shekara ta 1951 aka yi musu baftisma kuma wata shida bayan hakan suka soma yin hidimar majagaba. Sa’ad da nake ganawa da Mary, na lura cewa ita mai ibada ce sosai. Sai na cewa kaina, ‘Yarinya da zan so in aura ke nan.’ Wata tara bayan hakan, sai muka yi aure a ranar 30 ga Janairu a shekara ta 1954. Mako ɗaya bayan aurenmu an gayyace mu don a koya mana yadda ake hidimar mai kula da da’ira. Mun yi shekara biyu muna hidimar masu kula da da’ira a arewancin jihar Ontario.

Yayin da ake samun ƙaruwa sosai a wa’azi, an bukaci ‘yan’uwan da za su ba da kansu don su je wa’azi a ƙasar waje. Ni da Mary mun yi tunani sosai cewa idan za mu iya yin rayuwa a Kanada duk da yawan sanyin da ake yi a wajen da kuma sauron da ke wajen, ba abin da zai hana mu yin hidima a wasu wurare. A watan Yuli na shekara ta 1956 ne muka sauke karatu a Makarantar Gilead kuma mu ne ‘yan aji na 27, kuma muka je hidima a Brazil a watan Nuwamba.

SA’AD DA MUKE HIDIMA A BRAZIL

Da muka iso ofishinmu a Brazil, sai muka soma koyan yaren da ake yi a Portugal. Da muka koyi yadda za mu riƙa yin gaisuwa da kuma haddace yadda za mu gabatar da mujallunmu a cikin minti ɗaya, sai muka soma zuwa wa’azi. Idan muka haɗu da wanda yake son jin wa’azi, an faɗa mana mu bayyana masa yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da Mulkin Allah zai soma sarauta bisa duniya. A rana ta farko da muka soma fita wa’azi, wata mata ta saurare mu sosai, don haka na karanta mata littafin Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4 kuma bayan haka, sai na sume! Ban saba da ƙasa mai zafi kamar haka ba, kuma abin da zan riƙa fuskanta ke nan.

Mun yi hidima a birnin Campos dos Goytacazes a jihar Rio de Janeiro, kuma yanzu akwai ikilisiyoyi 15 a wajen. A lokacin da muka je wajen, rukuni ɗaya ne kawai a wurin da kuma gidan masu wa’azi a ƙasar waje. Ƙari ga haka, waɗanda suke zama a wajen su ne ‘yan’uwa mata guda huɗu masu suna Esther Tracy da Ramona Bauer da Luiza Schwarz da kuma Lorraine Brookes (yanzu Wallen). Aikina a gidan shi ne yin wanki da neman itacen da za a riƙa dahuwa da shi. Wata ranar Litinin bayan mu gama nazarin Hasumiyar Tsaro, matata ta kwanta a kan kujera muna hira, da ta ɗaga kanta sai ga maciji, kuma hakan ya jawo hayaniya sosai har sai da na kashe macijin!

Bayan mun koyi yaren da ake yi a Portugal na shekara ɗaya, sai na soma hidimar mai kula da da’ira a wajen. Mun sauƙaƙa rayuwarmu a wurin, ba wutan lantarki kuma muna kwanciya a kan tabarma. Ƙari ga haka, idan za mu yi tafiya, doki muke hawa. A lokacin da za mu je yin wa’azi a wajen da ba a yawan yin wa’azi, mukan yi tafiya ta jirgin ƙasa kuma mu yi hayar ɗaki. Ana tura mana mujallu guda 800 daga ofishinmu don yin wa’azi. Hakan ya sa muna yawan zuwa gidan waya don mu ɗauki mujallun.

A ƙasar Brazil, a shekara ta 1962 ne aka soma yin Makarantar Hidima ta Mulki don ‘yan’uwa maza da mata da suke wa’azi a ƙasar waje. Na yi wata shida ina koyar da ‘yan’uwa a makarantu dabam-dabam, amma ba tare da matata Mary ba. Na koyar a biranen Manaus da Belém da Fortaleza da Recife da kuma Salvador. Na shirya yadda za a yi taron yanki a babban gidan wasan opera da ke birnin Manaus. Ruwan sama ya ɓata wurin da muke dafa abinci da kuma ruwan da muke sha. A wannan lokacin ana ba da abinci a taron yanki. Na nemi taimakon wani soja kuma na gaya masa matsalar da muke ciki, sai ya sa aka kawo mana ruwan sha da muka yi amfani da shi a taron kuma ya turo sojoji su kafa wurin da za mu dafa abinci da kuma inda za mu riƙa cin abincin.

Idan na yi tafiya, matata Mary tana zuwa wa’azi a kasuwar ‘yan Portugal, amma a wannan kasuwar kuɗi kawai aka saka a gaba. Don haka, ba wanda yake sauraronta idan ta je wa’azi. Hakan ya sa ta gaya ma wasu ‘yan’uwa da ke Bethel cewa, “Ba zan so a tura ni Portugal don wa’azi ba.” Abin mamaki bayan hakan, ko da yake an hana aikinmu a ƙasar Portugal, mun sami wasiƙar zuwa ƙasar don yin hidima. Duk da cewa matata ba ta so hakan ba, mun je.

MUN YI HIDIMA A PORTUGAL

A watan Agusta a shekara ta 1964 ne muka iso birnin Lisbon da ke Portugal. ‘Yan sandan ciki suna tsananta wa ‘yan’uwanmu sosai a wajen kuma suna neman su. Don hakan ba mu nemi inda Shaidu suke sa’ad da muka isa wurin ba. Kafin mu sami izinin zama a ƙasar mun zauna a masauki. Da muka sami biza sai muka yi hayar gida. A watan Janairu a shekara ta 1965 ne muka tuntuɓi ofishinmu da ke wurin. Bayan wata biyar mun yi farin ciki sosai sa’ad da muka halarci taron ikilisiya.

Saboda an hana aikinmu a ƙasar, an rufe Majami’un Mulki kuma a gidan ‘yan’uwa ne ake yin taro. Ban da haka, ‘yan sanda suna yawan zuwa gidajen ‘yan’uwa don su yi bincike kuma su kai ‘yan’uwa da yawa da suka kama zuwa tashar ‘yan sanda don a yi musu tambayoyi. ‘Yan sandan suna wulaƙanta ‘yan’uwa sosai kuma suna tilasta musu su ba da sunayen ‘yan’uwan da ke gudanar da taro. Don su kāre juna ba sa yin amfani da sunayen mahaifin ‘yan’uwan, maimakon hakan, suna kiransu da ainihin sunayensu kamar su José da Paulo, sai mu ma muka soma yin hakan.

Taimaka wa ‘yan’uwa su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah ne ya fi muhimmanci a gare mu. Saboda haka, aikin da Mary take yi shi ne yin amfani da tafireta tana rubuta talifofin nazari na Hasumiyar Tsaro da wasu littattafai a kan wani irin takarda na musamman kuma ‘yan’uwa sun yi amfani da takardar don su yi kofofi da yawa.

YADDA MUKA KĀRE WA’AZIN DA MUKE YI A KOTU

A watan Yuni na shekara ta 1966 an yi wata shari’a babba a Lisbon. An kai ‘yan’uwa 49 da ke Ikilisiyar Feijó kotu don suna gudanar da taro a gida. Na ɗauki matsayin alƙali don na shirya su don karar da aka shigar a kotun, ina yi musu tambayoyi don in nuna suna da laifi. Ko da yake mun san cewa ba za mu yi nasara ba amma mun sa mutanen sun ji wa’azi. Lauyanmu ya kammala maganarsa ta wajen yin ƙaulin abin da Gamaliyal na ƙarni na farko ya ce. (A. M. 5:33-39) Masu yaɗa labarai sun faɗa abin da ya faru, kuma bayan haka aka yanke wa wasu cikin ‘yan’uwa guda 49 hukuncin yin kwanaki 45 a kurkuku wasu kuma wata biyar da sati biyu. Mun yi farin ciki cewa lauyanmu ya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro kafin mutuwarsa.

A watan Disamba na shekara ta 1966, na soma hidima a matsayin mai kula da ofishin Shaidun Jehobah kuma hakan ya sa na shiga harkar shari’a sosai. Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu ga cewa an ba wa Shaidun Jehobah ‘yanci yin ibada. (Filib. 1:7) Bayan haka, a ranar 18 ga Disamba na shekara ta 1974 gwamnatin ƙasar ta ba wa Shaidun Jehobah ‘yanci. ‘Yan’uwa Nathan Knorr da Frederick Franz daga hedkwatar Shaidun Jehobah sun ziyarci ƙasar Portugal don su yi taron da aka yi a birnin Oporto da kuma Lisbon tare da ‘yan’uwan kuma mutane 46,870 ne suka halarci taron.

Jehobah ya sa an yi wa’azi sosai a waɗannan yankunan da ke gaɓar teku kamar su Azores da Cape Verde da Madeira da São Tomé da kuma Príncipe. Mutane a waɗannan yankunan suna yaren da ake yi a Portugal. Ƙari ga haka, domin adadin ‘yan’uwa yana ƙaruwa sosai muna bukatar babban ofishi, saboda haka a shekara ta 1988 ne muka cim ma wannan. A ranar 23 ga Afrilu a wannan shekarar, ɗan’uwa Milton Henschel ya ba da jawabin keɓe ginin ga Jehobah kuma mutane 45,522 ne suka halarci taron. Kuma mun yi murnar marabtan ‘yan’uwan da suka yi hidima a ƙasar Portugal a dā da suka zo taron.

MUN AMFANA DAGA MISALIN ‘YAN’UWA MASU AMINCI

Yin cuɗanya da ‘yan’uwa masu aminci ya ƙarfafa mu sosai a hidimarmu. Ƙari ga haka, na koyi abubuwa sosai sa’ad da na yi aiki da ɗan’uwa Theodore Jaracz a lokacin da muka ziyarci wata ƙasa tare. ‘Yan’uwa a ofishin da muka je ziyara suna fuskantar wata matsala babba kuma kwamitin da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah a ƙasar ya yi iya ƙoƙarinsa don ya magance matsalar amma ya kasa. Ɗan’uwa Jaracz yana so ya kwantar musu da hankali don haka ya ce: “Yanzu ne ya kamata mu bar ruhu mai tsarki ya yi aikinsa.” Ƙari ga haka, ba zan taɓa manta da abin da Ɗan’uwa Franz ya faɗa shekaru da yawa da suka shige sa’ad da muka ziyarci Brooklyn ba. Sa’ad da ni da matata da wasu ‘yan’uwa muka ce masa ya ba mu shawara, sai ya ce mana: “Shawarar da zan ba ku ita ce, kada ku bar ƙungiyar Jehobah ko da me ya faru, saboda ita ce kawai take bin umurnin da Yesu ya bayar na yin wa’azin Mulkin Allah a dukan duniya!”

Bin wannan shawarar yana sa ni da matata farin ciki sosai. Ƙari ga haka, mun ji daɗin ziyarar ofisoshin Shaidun Jehobah da ke wasu ƙasashe. Hakan ya taimaka mana mu nuna wa ‘yan’uwa matasa da kuma tsofaffi yadda muke farin cikin ganin irin ƙwazo da suke da shi a hidimarsu ga Jehobah kuma mun ƙarfafa su su ci gaba da yin hakan.

Yanzu mun tsufa kuma shekarunmu tamanin ne da wani abu. Ƙari ga haka, Mary tana fama da rashin lafiya dabam-dabam. (2 Kor. 12:9) Mun fuskanci jaraba sosai, amma sun ƙarfafa bangaskiyarmu da kuma sa mu ƙuduri niyyar kasancewa da aminci. Idan muka tuna irin rayuwar da muka yi a hidimarmu ga Jehobah, hakika mun ga cewa Jehobah ya yi mana alheri sosai. *

^ sakin layi na 29 Ɗan’uwa Douglas Guest ya mutu a ranar 25 ga Oktoba a shekara ta 2015 yayin da ake shirin wallafa wannan labarin kuma ya kasance da aminci ga Jehobah har mutuwarsa.