Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 24

Mu Kawar da Kowane Ra’ayin da Ya Saba wa Na Allah!

Mu Kawar da Kowane Ra’ayin da Ya Saba wa Na Allah!

“Mun kawar da kowace muhawwara, muna rushe kowane abin da zai hana sanin Allah.”​—2 KOR. 10:5.

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya yi wa shafaffun Kiristoci?

MANZO BULUS ya yi gargaɗi cewa “kada ku yarda”! Yarda da mene ne? “Kada ku yarda tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinku.” (Rom. 12:2) Bulus ya rubuta waɗannan kalaman ne ga Kiristoci a ƙarni na farko. Me ya sa ya yi wa mata da maza shafaffu da suka yi alkawarin bauta wa Allah wannan gargaɗi?​—Rom. 1:7.

2-3. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin sa mu daina bauta wa Jehobah, amma yaya za mu iya kawar da halayen da ke da wuyan bari?

2 Bulus ya damu domin hikimar mutanen duniya da Shaiɗan yake ɗaukaka tana shafan wasu Kiristoci. (Afis. 4:​17-19) Hakan yana iya faruwa da mu a yau. Shaiɗan ne ke mulkin wannan duniyar. Don haka, yana yin amfani da dabaru da yawa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Alal misali, idan muna son mu yi arziki ko kuma suna, yana iya yin amfani da wannan sha’awa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, Shaiɗan yana iya yin amfani da abubuwan da muka koya a gida ko a makaranta ko kuma daga maƙwabtanmu don ya sa mu soma kasancewa da ra’ayinsa.

3 Zai yiwu mu kawar da halayen da muke da su da ke da wuyan bari kuwa? (2 Kor. 10:4) Ku ga amsar da Bulus ya ba da, ya ce: “Mun kawar da kowace muhawwara, muna rushe kowane abin da zai hana sanin Allah, muna kuma komo da kowane tunani zuwa ga bauta da biyayya ga Almasihu.” (2 Kor. 10:5) Da taimakon Jehobah, muna iya kawar da dukan halayenmu da ba su dace ba. Kamar yadda magani ke taimaka wa mutum don kada guba ta kashe shi, Kalmar Allah tana iya taimaka mana mu guji ra’ayin Shaiɗan da duniyarsa.

KU “SABUNTA TUNANINKU”

4. Waɗanne canje-canje ne da yawa a cikinmu muka yi sa’ad da muka koyi gaskiya?

4 Sa’ad da ka koyi gaskiyar da ke Kalmar Allah, ka yi canje-canje kuma ka yanke shawarar bauta wa Allah. Da yake muna son mu bauta wa Jehobah, da yawa daga cikinmu sun daina yin abubuwan da ba su dace ba. (1 Kor. 6:​9-11) Muna godiya don Jehobah ya taimaka mana mu kawar da halayen banza!

5. Waɗanne abubuwa biyu ne aka ambata a Romawa 12:2?

5 Amma kada mu ɗauka cewa ba ma bukatar mu ci gaba da yin canje-canje. Duk da cewa mun daina yin zunuban da muke yi kafin mu yi baftisma, muna bukatar mu mai da hankali don mu guji abubuwan da za su iya sa mu koma-gidan-jiya. Ta yaya za mu yi hakan? Bulus ya ba da amsar, ya ce: “Kada ku yarda tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinku, amma ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku.” (Rom. 12:2) Don haka, muna bukatar yin abubuwa biyu. Na farko, ‘Kada mu yarda’ hikimar wannan duniyar ta kama hankalinmu. Na biyu, muna bukatar mu “sabunta” tunaninmu ta wajen canja halayenmu.

6. Mene ne muka koya daga furucin Yesu a Matiyu 12:​43-45?

6 Ba canjin kamani kawai Bulus yake magana a kai ba. Amma canjin ya shafi dukan halayenmu. (Ka duba akwatin nan “ Mun Yi Canjin Gaske Ne Ko Na Ƙarya?”) Muna bukatar mu canja tunaninmu da hankalinmu da kuma sha’awarmu. Don haka, muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Canje-canjen da nake yi na gaske ne ko kuwa na munafunci ne?’ A furucin Yesu da ke littafin Matiyu 12:​43-45, ya faɗi abin da muke bukatar yi. (Karanta.) Waɗannan kalmomin sun koya mana darasi mai muhimmanci. Ba kawar da tunanin banza kawai muke bukatar yi ba, amma muna bukatar mu sauya su da ra’ayin da Allah ya amince da su.

KU “SABUNTA . . . HANKALINKU”

7. Ta yaya za mu sabunta tunaninmu da kuma hankalinmu?

7 Zai yiwu mu sabunta hankalinmu kuwa? Kalmar Allah ta ba da amsar. Ta ce: “Ya kamata a sabunta tunaninku da hankalinku. Ku ɗauki sabon halin nan da Allah ya halitta bisa ga kamannin kansa. Halin nan kuwa, ya bayyana cikin adalci da zaman tsarki.” (Afis. 4:​23, 24) Hakika, za mu iya sabunta hankalinmu, amma hakan bai da sauƙi. Ba guje wa sha’awoyin banza da kuma abubuwan da ba su dace kawai muke bukatar yi ba. Muna bukatar mu ‘sabunta . . . hankalinmu.’ Yin hakan ya ƙunshi canja sha’awarmu da halayenmu da kuma dalilan da suka sa muke yin wasu abubuwa. Muna bukatar yin aiki tuƙuru don yin waɗannan canje-canje.

8-9. Ta yaya labarin wani ɗan’uwa ya nuna mana dalilin da ya sa muke bukatar mu sabunta hankalinmu?

8 Alal misali, akwai wani da ke son yin faɗa sosai a dā da kuma buguwa da giya. Amma sai ya daina buguwa da giya da yin faɗa, kuma aka yi masa baftisma. Hakan ya sa mutanen yankinsu suka yabi Jehobah. Wata rana da yamma, bayan an yi masa baftisma, ya fuskanci jarrabawa. Wani mashayi ya zo gidansu don ya yi faɗa da shi. Da farko ɗan’uwan ya guji yin faɗa da mutumin. Amma sa’ad da mutumin ya ɓata sunan Jehobah, sai ɗan’uwan ya yi fushi kuma bai iya kame kansa ba. Ya fita ya yi wa mutumin dūkan tsiya. Me ya sa ya yi hakan? Ko da yake yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka masa ya guji son yin faɗa, bai sabunta hankalinsa ba.

9 Amma wannan ɗan’uwan ya ci gaba da yin canje-canje. (K. Mag. 24:16) Dattawa sun taimaka masa, kuma ya sami ci gaba sosai. A ƙarshe, ya zama datijo. Wata rana da yamma a wajen Majami’ar Mulki, ɗan’uwan ya fuskanci irin gwajin da ya fuskanta a dā. Wani mashayi yana so ya yi ma wani datijo dūka. Mene ne ɗan’uwan ya yi? Ya tattauna da mashayin a cikin kwanciyar hankali, har mashayin ya daina fushi, ban da haka, ya kai mutumin gida. Me ya sa ɗan’uwan ya bi da yanayin haka? Ya sabunta hankalinsa, ya zama mai tawali’u da mai son zaman lafiya, hakan ya kawo yabo ga Jehobah!

10. Mene ne yin canje-canje ya ƙunsa?

10 Waɗannan canje-canje ba sa faruwa haka kawai. Muna bukatar mu yi ‘iyakar ƙoƙarinmu’ har na tsawon shekaru da yawa. (2 Bit. 1:5) Waɗannan canje-canje ba za su faru don mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah ba. Muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu sabunta hankalinmu. Da akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi. Bari mu tattauna wasu daga cikinsu.

YADDA ZA MU CANJA HANKALINMU

11. Ta yaya yin addu’a za ta taimaka mana mu sabunta hankalinmu?

11 Wani abu mafi muhimmanci da muke bukatar yi shi ne addu’a. Muna bukatar yin addu’a kamar yadda wani marubucin Zabura ya yi. Ya ce: “Ya Allah, bari ka halicci zuciya marar ƙazanta a cikina, ka ba ni sabon ruhu da zuciya marar canjawa.” (Zab. 51:10) Zai dace mu fahimci cewa muna bukatar mu sabunta hankalinmu, kuma mu roƙi Jehobah ya taimaka mana. Mene ne zai tabbatar mana da cewa Jehobah zai taimaka mana mu yi canje-canje? Abin da Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi wa Isra’ilawa masu taurin kai a zamanin Ezekiyel zai ƙarfafa mu. Ya ce: “Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu . . . in ba su zuciya mai laushi, [wato zuciyar da za ta riƙa bin ja-goranci Allah].” (Ezek. 11:19) Jehobah ya kasance a shirye ya taimaka wa Isra’ilawa su canja halayensu, kuma yana a shirye ya taimaka mana.

12-13. (a) Kamar yadda Zabura 119:59 ta nuna, mene ne muke bukatar yin bimbini a kai? (b) Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu yi wa kanmu?

12 Yin bimbini shi ne abu na biyu da muke bukatar mu yi. A kowace rana sa’ad da muke karanta Kalmar Allah, muna bukatar mu keɓe lokaci don mu yi bimbini a kan halayenmu da muke bukatar mu canja. (Karanta Zabura 119:59; Ibran. 4:12; Yaƙ. 1:25) Muna bukatar mu bincika kanmu don mu san ko muna sha’awar bin hikimar mutanen duniya. Ya kamata mu san cewa muna da kasawa domin hakan zai taimaka mana mu yi aiki tuƙuru don mu kawar da su.

13 Alal misali, ka tambayi kanka: ‘Ni mai kishi ne?’ (1 Bit. 2:1) ‘Ina gani cewa na fi wasu daraja don ƙabilata ko ilimina ko kuma arzikina?’ (K. Mag. 16:5) ‘Shin ina rena mutanen da ba su da abin da nake da shi ko kuma da suka fito daga wani wuri dabam?’ (Yaƙ. 2:​2-4) ‘Ina son abubuwan da ke wannan duniyar?’ (1 Yoh. 2:​15-17) ‘Ina jin daɗin yin nishaɗin da ake lalata da kuma zalunci?’ (Zab. 97:10; 101:3; Amos 5:15) Amsoshin waɗannan tambayoyin suna iya taimaka mana mu san irin canjin da muke bukata. Idan muka canja halayen da suka zama mana jiki, za mu faranta ran Ubanmu da ke sama.​—Zab. 19:14.

14. Me ya sa muke bukatar mu zaɓi abokan kirki?

14 Abu na uku da muke bukata shi ne zaɓar abokan kirki. Ko mun ƙi ko mun so, halayen abokanmu suna shafan mu sosai. (K. Mag. 13:20) Wataƙila muna cuɗanya da mutane a wurin aiki ko kuma a makaranta da ba za su taimaka mana mu riƙa faranta ran Allah ba. Amma za mu iya samun abokan kirki a ikilisiya. A wurin ne za mu sami ƙarfafa don “nuna ƙauna da yin aikin nagarta.”​—Ibran. 10:​24, 25.

KU ‘TSAYA A KAN BANGASKIYARKU’

15-16. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya canja tunaninmu?

15 Mu tuna cewa Shaiɗan yana yin ƙoƙari ya canja tunaninmu. Yana yin amfani da koyarwa dabam-dabam don ya sa mu ƙi abubuwan da muka koya daga Kalmar Allah.

16 Har a yau, Shaiɗan yana yin amfani da irin tambayar da ya yi wa Hauwa’u a lambun Adnin. Ya ce: Da gaske ne “Allah ya ce . . . ?” (Far. 3:1) A duniyar nan da Shaiɗan ke mulki, muna yawan jin tambayoyi kamar: ‘Da gaske ne Allah ba ya so mu auri mata da yawa? Da gaske ne Allah ba ya son mu riƙa yin bikin Kirsimati da na ranar haihuwa? Da gaske ne Allahnku ba ya so ku karɓi ƙarin jini? Da gaske ne Allah mai ƙauna ba ya son mu yi cuɗanya da ’yan’uwan da aka yi musu yankan zumunci?’

17. Me ya kamata mu yi idan wani ya yi mana tambaya don ya sa mu yi shakkar imaninmu, kuma wane sakamako ne Kolosiyawa 2:​6, 7 ya ce za mu iya samu?

17 Muna bukatar mu tabbata da abubuwan da muka yi imani da su. Idan ba mu sami amsoshin tambayoyi masu muhimmanci ba, hakan zai iya sa mu soma shakkar abin da muka yi imani da shi. Irin wannan shakkar za ta canja tunaninmu kuma ta sa mu ɓata dangantakarmu da Allah. Mene ne muke bukatar yi? Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu sabunta hankalinmu. Yin hakan zai tabbatar mana cewa muna yin “abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.” (Rom. 12:2) Ta wajen yin nazari a kai a kai za mu tabbatar wa kanmu cewa abin da muke koya a Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. Za mu kasance da tabbaci cewa mizanan Jehobah sun dace sosai. Idan muka yi hakan, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi.​—Karanta Kolosiyawa 2:​6, 7.

18. Mene ne zai taimaka mana mu kāre kanmu daga rinjayar Shaiɗan?

18 Mu ne za mu iya sa bangaskiyarmu ta yi ƙarfi. Don haka, mu ci gaba da sabunta hankalinmu. Mu riƙa addu’a a kai a kai, mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Mu riƙa yin bimbini kuma mu riƙa daidaita tunaninmu da kuma muradinmu. Ƙari ga haka, mu nemi abokan kirki waɗanda za su taimaka mana mu sabunta hankalinmu. Ta wajen yin waɗannan abubuwan, za mu kāre kanmu daga Shaiɗan da dabarunsa kuma za mu kawar da kowane ra’ayin da ya saɓa wa na Allah.​—2 Kor. 10:5.

WAƘA TA 50 Alkawarin Bauta wa Jehobah

^ sakin layi na 5 Yadda aka rene mu da al’adarmu da kuma iliminmu suna shafan tunaninmu da ra’ayinmu. Muna iya lura cewa muna da wani halin da bai dace ba. Wannan talifin zai nuna mana yadda za mu iya kawar da dukan halayenmu da ba su dace ba.