Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Wa’azi Game da Alherin Allah

Ka Yi Wa’azi Game da Alherin Allah

Ka “shaida bishara ta alherin Allah.”A. M. 20:24.

WAƘOƘI: 101, 84

1, 2. Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa yana godiya don alherin da Allah ya nuna masa?

MANZO BULUS ya ce: ‘Alherin Allah fa da aka bayar a gareni ba ya zama banza ba.’ (Karanta 1 Korintiyawa 15:9, 10.) Bulus ya sani sarai cewa tun da yake ya tsananta wa Kiristoci a dā bai cancanci Allah ya nuna masa alheri ba.

2 Lokacin da Bulus ya kusan gama hidimarsa a duniya, ya rubuta wa Timotawus abokin aikinsa cewa: “Ina godiya ga wanda ya ba ni iko, watau Kristi Yesu Ubangijinmu, da ya aza ni amintacce, har ya sanya ni ga aikinsa.” (1 Tim. 1:12-14) Wane aiki ne wannan? Bulus ya gaya wa dattawan da ke ikilisiyar Afisa abin da hakan ya ƙunsa, ya ce: ‘Amma ban mai da raina wani abu ba, kamar abin tamani a gareni, bisa ga in cika tafiyata, da hidima kuma wadda na karɓa daga wurin Ubangiji Yesu, in shaida bishara ta alherin Allah ke nan.’A. M. 20:24.

3. Wane aiki na musamman ne aka ce Bulus ya yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 26.)

3 Wace “bishara” ce Bulus ya yi da ta nuna alherin Jehobah? Ya gaya wa Kiristoci da ke Afisa cewa: “Kun ji labarin wakilcin alherin nan na Allah da aka ba ni dominku.” (Afis. 3:1, 2) An gaya wa Bulus ya yi wa waɗanda ba Yahudawa ba wa’azin bishara. Hakan zai sa mutane daga wasu al’ummai su yi sarauta da Yesu a Mulkin Allah. (Karanta Afisawa 3:5-8.) Bulus ya yi wa’azi da ƙwazo kuma ya kafa wa Kiristoci a yau misali mai kyau. Ta hakan ya nuna cewa alherin da Allah ya nuna masa ba a “banza ba” ne.

ALHERIN ALLAH YANA MOTSA KA KA YI WA’AZI?

4, 5. Me ya sa muka ce ‘bishara ta mulki’ ɗaya ne da “bishara ta alherin Allah”?

4 A wannan kwanaki na ƙarshe, an gaya wa mutanen Jehobah su yi ‘bishara ta mulki . . . cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.’ (Mat. 24:14) Wa’azin da muke yi ɗaya ne da “bishara ta alherin Allah.” Alherin da Jehobah ya nuna mana ta hanyar Kristi ne zai sa mu sami dukan albarkar da muke begensu a Mulkin Allah. (Afis. 1:3) Shin kowannen mu yana yin koyi da Bulus wajen yin bishara da ƙwazo don ya gode wa Jehobah domin alherinsa?—Karanta Romawa 1:14-16.

5 A talifin da ya gabata, mun koyi yadda muke amfana daga alherin Jehobah a hanyoyi da yawa duk da cewa mu masu zunubi ne. Saboda haka, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu gaya wa dukan mutane game da yadda Jehobah yake nuna ƙaunarsa da kuma yadda su ma za su amfana daga alherinsa. Waɗanne fannoni na alherin Allah ne ya kamata mu taimaka wa mutane su sani?

KA YI WA’AZI GAME DA FANSAR YESU

6, 7. Ta yaya muke yaɗa bishara ta alherin Allah sa’ad da muka bayyana wa mutane ma’anar fansa?

6 A yau, mutane da yawa ba sa damuwa sa’ad da suka yi zunubi, domin ba su fahimci dalilin da ya sa ’yan Adam suke bukatar fansa ba. Duk da haka, mutane suna daɗa ganin cewa salon rayuwarsu ba ya sa su farin ciki. Sa’ad da mutane suka tattauna da Shaidun Jehobah ne suke fahimtar ma’anar zunubi, da yadda yake shafan mu, da kuma abin da muke bukatar mu yi don a cece mu daga zunubi. Mutane masu zuciyar kirki suna farin ciki sosai sa’ad da suka koyi cewa Jehobah ya turo Ɗansa zuwa duniya don ya ’yantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Jehobah ya yi hakan don alherinsa da kuma ƙaunar da yake mana.—1 Yoh. 4:9, 10.

7 Sa’ad da Bulus yake magana game da Ɗan Jehobah ƙaunatacce, ya ce: “Muna da fansarmu a cikinsa [Yesu] ta wurin jininsa, [wato] gafarar laifofinmu, gwargwadon wadatar alherinsa [Jehobah].” (Afis. 1:7) Allah yana ƙaunarmu sosai shi ya sa ya turo Kristi ya mutu a madadinmu, kuma hakan ya nuna cewa Allah mai alheri ne. Muna samun kwanciyar hankali sa’ad da muka koyi cewa idan muka ba da gaskiya ga hadayar Yesu, za a gafarta mana zunubanmu kuma za mu kasance da lamiri mai kyau! (Ibran. 9:14) Hakika, ya dace mu sanar da mutane game da wannan bisharar!

KA TAIMAKA WA MUTANE SU ƘULLA DANGANTAKA DA ALLAH

8. Me ya sa ’yan Adam masu zunubi suke bukatar su sulhunta da Allah?

8 Muna da hakkin sanar da mutane cewa za su iya ƙulla dangantaka na kud da kud da Mahaliccinsu. Allah yana ɗaukan ’yan Adam a matsayin maƙiyansa idan ba su ba da gaskiya ga hadayar Yesu ba. Manzo Yohanna ya ce: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda bai bada gaskiya ga Ɗan ba, ba zai gan rai ba, amma fushin Allah yana bisansa zaune.” (Yoh. 3:36) Muna farin ciki cewa hadayar Kristi ta sa mun zama abokan Allah. Bulus ya ce: “Ku kuma, da kuke dā rababbu ne, magabta ne kuma cikin hankalinku ga wajen munanan ayyukanku, duk da wannan yanzu ya sulhunta ku cikin jiki na namansa ta wurin mutuwa, domin shi miƙa ku tsarkaka, marasa-aibi, marasa-abin zargi a gabansa.”—Kol. 1:21, 22.

9, 10. (a) Wane hakki ne Kristi ya ba ’yan’uwansa shafaffu? (b) Ta yaya “waɗansu tumaki” suke taimaka wa ’yan’uwansu shafaffu?

9 Kristi ya ba ’yan’uwansa shafaffu a duniya “hidima ta sulhu.” Sa’ad da Bulus yake bayyana hakan, ya rubuta wa shafaffu Kiristoci na ƙarni na farko cewa: “Abu duka na Allah ne, wanda ya sulhunta mu ga kansa ta wurin Kristi, har ya ba mu hidima ta sulhu; wato, Allah yana cikin Kristi yana sulhunta duniya zuwa kansa, ba ya lissafta laifofinsu a gare su ke nan, ya kuma damƙa mana maganar sulhu. Mu fa manzanni ne madadin Kristi, sai ka ce Allah yana yin roƙo ta wurinmu: muna roƙonku madadin Kristi, ku sulhuntu ga Allah.”—2 Kor. 5:18-20.

10 “Waɗansu tumaki” suna ganin cewa babban gata ne su taimaka wa ’yan’uwansu shafaffu a wannan hidimar. (Yoh. 10:16) A matsayinsu na wakilan Kristi, su ne suka fi yin wa’azi, suna koya wa mutane game da Jehobah kuma suna taimaka musu su ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi. Wannan sashe ne mai muhimmanci a wa’azin da muke yi game da alherin Allah.

KA KOYA WA MUTANE CEWA ALLAH YANA JIN ADDU’O’INMU

11, 12. Me ya sa yake da kyau mutane su koya cewa za su iya yin addu’a ga Jehobah?

11 Mutane da yawa suna yin addu’a ne kawai don yana sa su farin ciki, amma ba su gaskata cewa Allah yana jin addu’o’insu ba. Suna bukatar su sani cewa Jehobah “mai jin addu’a” ne. Dauda marubucin wannan zaburar ya ce: “Ya mai jin addu’a, a gareka dukan masu rai za su zo. Al’amura na kurakurai sun yi nasara da ni: Don laifofinmu fa, za ka shafe su.”—Zab. 65:2, 3.

12 Yesu ya gaya wa almajiransa: ‘Idan kun roƙe ni kome a cikin sunana, [“zan yi shi,” NW]’ (Yoh. 14:14) Hakika “kome” yana nufin duk wani abin da ya yi daidai da nufin Jehobah. Yohanna ya gaya mana cewa: “Gaba gaɗi ke nan da muke yi a gabansa, idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jinmu.” (1 Yoh. 5:14) Yana da kyau mu taimaka wa mutane su san cewa addu’a ba kawai abin da ke sa mu farin ciki ba ne amma hanya ce da muke kusantar “kursiyi na alherin” Jehobah. (Ibran. 4:16) Idan muka koya wa mutane yadda za su yi addu’a ga Allah, kuma muka koya musu abubuwan da ya kamata su roƙa, za mu taimaka musu su kusaci Jehobah kuma su sami ƙarfafawa sa’ad da suke shan wahala.—Zab. 4:1; 145:18.

ZA A NUNA MANA ALHERI A SABUWAR DUNIYA

13, 14. (a) Wane babban gate ne shafaffu za su samu a nan gaba? (b) Wane aiki mai ban al’ajabi ne shafaffu za su yi wa ’yan Adam?

13 Jehobah zai nuna alherinsa sosai a sabuwar duniya. Allah ya ba wa mutane 144,000 gatan yin sarauta da Kristi a Mulkin sama. Bulus ya bayyana hakan sa’ad da ya ce: “Allah, domin mawadaci ne cikin jinƙai, saboda ƙaunarsa mai-yawa wadda ya ƙaunace mu da ita, ko lokacin da muke matattu ta wurin laifofinmu, ya rayar da mu tare da Kristi ta wurin alheri an cece ku, ya tashe mu tare da shi, ya zamshe mu tare da shi cikin sammai, cikin Kristi Yesu: Domin cikin zamanu masu-zuwa shi bayyana mafificiyar wadatar alherinsa cikin nasiha zuwa gare mu cikin Kristi Yesu.”—Afis. 2:4-7.

14 Ba za mu iya kwatanta yawan abubuwa masu ban al’ajabi da Jehobah zai yi wa shafaffu sa’ad da suka soma sarauta da Kristi a sama ba. (Luk. 22:28-30; Filib. 3:20, 21; 1 Yoh. 3:2) Jehobah zai nuna musu “mafificiyar wadatar alherinsa.” Za su kasance cikin “sabuwar Urushalima,” wato amaryar Kristi. (R. Yoh. 3:12; 17:14; 21:2, 9, 10) Za su ‘warkar da al’ummai’ tare da Yesu. Ƙari ga haka, za su ’yantar da ’yan Adam masu biyayya daga zunubi da mutuwa kuma su zama kamiltattu.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2, 17.

15, 16. Ta yaya Jehobah zai nuna alherinsa ga “waɗansu tumaki” a nan gaba?

15 Littafin Afisawa 2:7 ta ce, Allah zai nuna alherinsa “a cikin zamani mai-zuwa.” Babu shakka, mutanen da za su yi rayuwa a cikin sabuwar duniya za su shaida “mafificiyar wadatar alherinsa.” (Luk. 18:29, 30) Ɗaya daga cikin hanyoyin da Jehobah zai nuna alherinsa ita ce, zai ta da ’yan Adam daga mutuwa. (Ayu. 14:13-15; Yoh. 5:28, 29) Za a ta da mutanen dā da suka kasance da aminci kuma suka mutu kafin Kristi ya ba da hadayar fansa. Kuma za a ta da “waɗansu tumaki” masu aminci da suka mutu a wannan kwanaki na ƙarshe don su ci gaba da bauta wa Jehobah.

16 Ƙari ga haka, za a ta da miliyoyin ’yan Adam da suka mutu da ba su san Allah ba. Za a ba su zarafin goyon bayan sarautar Jehobah. Yohanna ya ce: “Na ga matattu kuma, ƙanana da manya, suna tsaye a gaban kursiyin; aka buɗe littattafai: aka buɗe wani littafi kuma, littafin rai ke nan: aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abin da aka rubuta cikin littattafai, gwargwadon ayyukansu. Teku kuma ya ba da matattun da ke cikinsa; mutuwa da Hades kuma suka ba da matattun da ke cikinsu: aka yi musu shari’a kuma, kowane mutum gwargwadon ayyukansa.” (R. Yoh. 20:12, 13) Hakika, za a koya wa waɗanda aka ta da daga mutuwa yadda za su bi ƙa’idodin Jehobah da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, za su bi sababbin umurnin da aka bayyana a cikin “littattafai” da kuma ƙa’idodin Jehobah game da yin rayuwa a sabuwar duniya. Waɗannan sababbin umurnin wata hanya ce da Jehobah zai nuna alherinsa.

KA CI GABA DA YIN WA’AZI

17. Mene ne ya kamata mu riƙa tunawa sa’ad da muke wa’azin bishara?

17 Yanzu ne ya fi muhimmanci mu yi wa’azi game da Mulkin Allah domin ƙarshen ya kusa! (Mar. 13:10) Babu shakka, wa’azin da muke yi yana nuna alherin Jehobah. Ya kamata mu riƙa tuna da hakan sa’ad da muke wa’azi. Muna yin wa’azi don mu ɗaukaka Jehobah. Muna bukatar mu gaya wa mutane cewa alherin Jehobah ne zai sa su sami albarka sosai a sabuwar duniya.

Ku yi wa’azi da ƙwazo a matsayinku na “nagargarun wakilai na alherin Allah.”—1 Bit. 4:10 (Ka duba sakin layi na 17-19)

18, 19. Ta yaya muke ɗaukaka alherin Jehobah?

18 Sa’ad da muke wa mutane wa’azi, za mu iya bayyana musu cewa dukan ’yan Adam za su amfana sosai daga hadayar fansar Yesu Kristi sa’ad da zai soma sarauta, kuma a hankali za su zama kamiltattu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ana bege halitta da kanta kuma za ta tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.” (Rom. 8:21) Hakan zai yiwu ne kawai domin alherin Jehobah.

19 Muna da gatan gaya wa mutane alkawarin da ke cikin Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5 cewa: “[Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” Ƙari ga haka, Jehobah wanda yake zaune a kan kursiyin ya ce: “Duba, sabonta dukan abu ni ke yi. Ya ce kuma, ka rubuta: Gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.” Hakika, muna ɗaukaka alherin Jehobah sa’ad da muke wa mutane wa’azi da ƙwazo!