Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Ci Gaba da ‘Yin Tsaro’?

Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Ci Gaba da ‘Yin Tsaro’?

“Gama ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa.”—MAT. 24:42.

WAƘOƘI: 136, 129

1. Wane misali ne ya nuna muhimmancin yin tsaro da kuma sanin abubuwan da suke faruwa. (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

LOKACIN soma sashe na gaba na taron yanki ya kusa. Mai kujerar sashe ya hau kan bagadi kuma ya marabci masu sauraro. Za a soma kaɗe-kaɗe. ’Yan’uwa sun san cewa lokaci ya yi da za su nemi wuri su zauna don su saurari kaɗe-kaɗe masu daɗi da aka shirya da kuma jawaban da za a bayar. Amma idan hankalin wasu ’yan’uwa ya rabe fa, suna yawo ko kuma suna tattaunawa da abokansu a wannan lokacin? Hakan ya nuna cewa ba sa kasancewa a faɗake kuma ba su lura da abin da yake faruwa ba, wato, mai kujera ya hau kan dakalin magana kuma an soma kaɗe-kaɗe. Ƙari ga haka, lokaci ne da ya kamata su zauna. Wannan misalin zai taimaka mana mu fahimci abin da zai faru a nan gaba da kuma dalilin da ya sa ya wajaba mu yi shiri don abin da zai faru. Mene ne wannan abin?

2. Me ya sa Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su ci gaba da ‘yin tsaro’?

2 Sa’ad da Yesu Kristi yake magana game da “cikar zamani,” ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku yi lura, ku yi tsaro, . . . gama ba ku san lokacin da sa’a take ba.” Bayan haka, sai Yesu ya ci gaba da gaya musu a kai a kai cewa: “Ku yi tsaro.” (Mat. 24:3; karanta Markus 13:32-37.) Littafin Matta ya bayyana cewa Yesu ya ci gaba da yi wa mabiyansa wannan gargaɗin: ‘Ku yi tsaro fa: gama ba ku san ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa ba. . . . Ku fa ku zama da shiri: gama cikin sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.’ Sai ya ƙara cewa: ‘Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.’—Mat. 24:42-44; 25:13.

3. Me ya sa muke ɗaukan gargaɗin Yesu da muhimmanci?

3 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna ɗaukan wannan gargaɗin Yesu da muhimmanci. Mun san cewa muna rayuwa ne a “kwanakin ƙarshe” kuma “ƙunci mai-girma” yana gab da somawa! (Dan. 12:4; Mat. 24:21) Muna ganin yaƙe-yaƙe a duniya, lalata da mugunta sai ƙaruwa suke yi, addinai suna ƙara ruɗar da mutane, ga kuma rashin abinci da cututtuka da kuma girgizar ƙasa. Ƙari ga haka, mun san cewa mutanen Allah a ko’ina suna wa’azin bishara. (Mat. 24:7, 11, 12, 14; Luk. 21:11) Muna jiran lokacin da Yesu zai zo ya cika nufin Allah.—Mar. 13:26, 27.

RANAR TANA GABATOWA

4. (a) Me ya sa muka gaskata cewa yanzu Yesu ya san lokacin da yaƙin Armageddon zai fara? (b) Wane tabbaci muke da shi duk da cewa ba mu san lokacin da za a fara ƙunci mai girma ba?

4 Mun san cewa an keɓe lokacin da za a fara kowane taron yanki. Amma, kome ƙoƙarin da muka yi, ba za mu san ainihin lokacin da za a fara ƙunci mai girma ba. Sa’ad da Yesu yake duniya, ya ce: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” (Mat. 24:36) Amma an riga an ba Yesu iko a sama don ya yaƙi duniyar Shaiɗan. (R. Yoh. 19:11-16) Saboda da haka, za mu iya cewa yanzu Yesu ya san lokacin da za a fara yaƙin Armageddon. Amma mu ba mu sani ba. Shi ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da yin tsaro har sai an soma ƙunci mai girma. Jehobah ya riga ya san lokacin da ƙarshen duniyar nan zai zo kuma lokacin yana gabatowa, “ba za ta yi jinkiri ba.” (Karanta Habakkuk 2:1-3.) Ta yaya muka sani?

5. Ka ba da misalin da ya nuna cewa annabce-annabcen da Jehobah ya yi suna cika a kan lokaci.

5 Annabce-annabcen da Jehobah ya yi suna cika a kan lokaci. Ka yi la’akari da ranar da ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Hakan ya faru ne a ranar 14 ga Nisan a shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu. Game da wannan ranar, Musa ya ce: ‘A ƙarshen shekarun nan arbaminya da talatin, a waccan rana fa, sai ya zama dukan rundunan Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.’ (Fit. 12:40-42) Waɗannan shekarun “arbaminya da talatin” sun soma ne sa’ad da Jehobah ya cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim a shekara ta 1943 kafin haihuwar Yesu. (Gal. 3:17, 18) Daga baya, Jehobah ya gaya wa Ibrahim: “Sai ka sani lallai zuriyanka za su yi baƙonci a cikin ƙasa wadda ba tasu ba ce, za su yi masu bauta kuma; za su gwada masu wuya kuma shekara arbaminya.” (Far. 15:13; A. M. 7:6) Wannan “shekara arbaminya” ta soma ne a shekara ta 1913 kafin haihuwar Yesu sa’ad da Isma’ila ya soma yi wa Ishaku ba’a kuma shekarar ta ƙare sa’ad da Isra’ilawa suka bar ƙasar Masar a shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu. (Far. 21:8-10; Gal. 4:22-29) Hakika, da daɗewa Jehobah ya riga ya ƙayyade ainihin lokacin da zai ceci mutanensa!

6. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai ceci mutanensa?

6 Joshua, wanda yake cikin waɗanda suka tsira daga ƙasar Masar ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga ciki.” (Josh. 23:2, 14) Mu ma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi cewa zai cece mu daga ƙunci mai girma. Amma idan muna so mu tsira daga ƙunci mai girma, wajibi ne mu kasance a faɗake.

KASANCEWA A SHIRYE ZAI SA MU TSIRA

7, 8. (a) A zamanin dā, mene ne aikin masu tsaro, kuma wane darasi ne hakan yake koya mana? (b) Ka ba da misalin abin da zai iya faruwa idan masu tsaro suka yi barci a bakin aiki.

7 Za mu iya koyan darasi game da muhimmancin yin tsaro daga yadda ake yin tsaro a dā. A lokacin, ana kewaye manyan birane kamar Urushalima da garuka masu tsayi. Masu tsaro suna tsayawa a kan waɗannan garukan kuma daga wurin, suna iya ganin duka yankunan da ke kusa da birnin. Wasu kuma suna yin tsaro a kofar birnin dare da rana. Waɗannan masu tsaron suna bukatar su kasance a faɗake kuma idan suka hangi cewa maƙiya suna zuwa, suna sanar da mutanen da suke cikin birnin. (Isha. 62:6) Sun san cewa yana da muhimmanci su kasance a faɗake kuma su san abubuwan da suke faruwa. Idan ba su yi hakan ba, mutane da yawa za su iya mutuwa.—Ezek. 33:6.

8 Wani marubucin tarihi mai suna Josephus, ya bayyana yadda Romawa suka shiga cikin birnin Urushalima a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu. Waɗanda suke tsaron birnin sun yi barci, hakan ya ba sojojin Romawa damar shiga birnin. Sun shiga cikin haikalin, suka cinna mata wuta kuma suka halaka sauran birnin Urushalima. Wannan shi ne ƙunci mafi girma da mutanen Yahudawa suka taɓa fuskanta.

9. Mene ne yawancin mutane a yau ba su sani ba?

9 Yawancin ƙasashe a yau suna amfani da “masu tsaro” a iyakar ƙasarsu kuma suna yin amfani da na’urorin tsaro don su kāre ƙasarsu. Waɗannan masu tsaron suna lura da duk wani abin da zai iya yin barazana ga tsaron ƙasarsu. Waɗannan “masu tsaro” suna iya kāre kansu daga ’yan Adam da kuma gwamnatocin ’yan Adam kawai. Amma ba su san cewa Mulkin Allah ya soma sarauta a sama ba kuma sarki Yesu ne zai hukunta dukan al’ummai nan ba da daɗewa ba. (Isha. 9:6, 7; 56:10; Dan. 2:44) Amma idan muka kasance a faɗake kuma muka ƙarfafa dangantakarmu da Allah, za mu kasance a shirye sa’ad da wannan ranar hukunci ta zo.—Zab. 130:6.

KADA KA YARDA WANI ABU YA RABA HANKALINKA

10, 11. (a) Mene ne za mu mai da hankali a kai kuma me ya sa? (b) Mene ne ya tabbatar maka cewa Shaiɗan yana rinjayar mutane don kada su saurari wa’azin da muke yi game da ƙarshen duniya?

10 Ka yi tunani game da mai tsaron da ya kasance a faɗake har asuba. Amma ya gaji, sai ya soma jin barci sa’ad da gari ya kusan wayewa. Hakazalika, yayin da ƙarshen wannan zamanin yake gabatowa, zai yi mana wuya mu zauna a faɗake. Idan ba mu kasance a faɗake a wannan lokacin ba, hakan zai kasance da haɗari sosai! Bari mu tattauna wasu abubuwa guda uku da za su iya hana mu kasancewa a faɗake, idan ba mu mai da hankali ba.

11 Shaiɗan yana rinjayar mutane don kada su ji wa’azin bishara. Kafin Yesu ya mutu, ya gargaɗi almajiransa sau uku game da “mai-mulkin wannan” duniyar. (Yoh. 12:31; 14:30; 16:11) Yesu ya san cewa Shaiɗan zai sa mutane su ƙi jin wa’azin bishara kuma zai hana su fahimtar annabcin da Allah ya yi game da abubuwan da za su faru a nan gaba. (Zaf. 1:14) Yana amfani ne da addini ƙarya. Mene ne ka lura da shi sa’ad da kake magana da mutane? Ka lura cewa Shaiɗan ya riga ya “makantar da hankalinsu” game da ƙarshen wannan zamanin da kuma cewa yanzu Yesu yana Mulki a sama? (2 Kor. 4:3-6) Sau nawa ne kake jin mutane suna cewa, “Ba na so na saurari wa’azinku”? A yawancin ƙasashe, mutane ba sa so su saurare mu sa’ad da muke gaya musu cewa ƙarshe ya kusa kuma Yesu yana mulki a sama.

12. Me ya sa bai kamata mu bar Shaiɗan ya rinjaye mu ba?

12 Kada ka bar abubuwan da mutane suke yi ya sa ka karaya ko kuma ya hana ka kasancewa a faɗake. Ka san cewa kasancewa a faɗake yana da muhimmanci. Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa cewa: “Ku da kanku kun sani sarai ranar Ubangiji tana zuwa,” kuma ya daɗa cewa kamar “ɓarawo da dare.” (Karanta 1 Tasalonikawa 5:1-6.) Yesu ya gargaɗe mu: “Ku yi shiri: gama cikin sa’a da ba ku sa tsammani ba, Ɗan mutum yana zuwa.” (Luk. 12:39, 40) Nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan zai rinjayi mutane su gaskata cewa za a sami “kwanciyar rai da lafiya” a duniya. Zai sa su soma tunanin cewa duniya ta soma gyaruwa. Mu kuma fa? Kada mu bar “ranan nan . . . ta tarshe [mu] kamar ɓarawo.” Saboda haka, mu zauna a faɗake. Shi ya sa kowace rana, muna bukatar mu riƙa karanta Kalmar Allah kuma mu yi bimbini a kan abubuwan da Jehobah yake gaya mana.

13. Ta yaya tasirin wannan duniyar yake shafan ra’ayin mutane a yau, kuma ta yaya za mu guji hakan?

13 Tasirin wannan duniyar yana hana mutane su kasance a faɗake. Mutane da yawa sun mai da hankali ga biɗan abin duniya kuma hakan ya sa suna ganin cewa ba sa “bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Mat. 5:3, NW) Suna amfani da lokacinsu da kuzarinsu don su biɗi “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu.” (1 Yoh. 2:16) Ƙari ga haka, ’yan talla suna sa mutane su so “annishuwa” kuma hakan yana ƙaruwa a kowace shekara. (2 Tim. 3:4) Shi ya sa Bulus ya gargaɗi Kiristoci cewa kada kuwa su yarda su bi ‘sha’awoyin’ jiki wanda zai iya sa mutum ba zai kasance a faɗake ba.—Rom. 13:11-14.

14. Wane gargaɗi ne Yesu ya bayar a littafin Luka 21:34, 35?

14 Maimakon mu bi ra’ayin wannan duniyar, muna barin ruhu Allah ya ja-gorance mu. Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya sa mu fahimci abubuwan da za su faru a nan gaba. [1] (1 Kor. 2:12) Duk da haka, muna bukatar mu yi hattara, domin kada wani abin da bai taka kara ya karya ba ya hana mu kasancewa a faɗake. (Karanta Luka 21:34, 35.) Wasu suna iya yi mana ba’a don mun gaskata cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe, amma kada mu bar wani abu ya hana mu kasancewa a faɗake. (2 Bit. 3:3-7) Maimakon haka, wajibi ne mu riƙa tarayya da ’yan’uwanmu a taron ikilisiya don a wurin ne ruhun Allah yake.

Shin kana yin iya ƙoƙarinka don ka kasance a faɗake? (Ka duba sakin layi na 11-16)

15. Mene ne ya faru da Bitrus da Yakub da Yohanna, kuma ta yaya hakan zai iya faruwa da mu?

15 Da yake mu ajizai ne, hakan zai iya hana mu kasancewa a faɗake. Yesu ya san cewa ’yan Adam ajizai ne, shi ya sa yake musu sauƙi su bi sha’awoyi na jiki. Ka yi la’akari da abin da ya faru a dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu. Yesu ya bukaci taimako daga wurin Ubansa na sama don ya kasance da aminci. Yesu ya gaya wa Bitrus da Yakub da Yohanna cewa su “yi tsaro” sa’ad da zai je yin addu’a. Amma ba su fahimci muhimmancin abin da zai faru a lokacin ba. Maimakon su yi tsaro tare da Ubangijinsu, sai suka yi barci. Ko da yake Yesu ya gaji sosai, ya kasance a faɗake kuma ya ci gaba da yin addu’a ga Ubansa. Abin da ya kamata almajiransa su yi ke nan.—Mar. 14:32-41.

16. Bisa ga littafin Luka 21:36, ta yaya Yesu ya umurce mu mu ci gaba da ‘yin tsaro’?

16 Me zai taimaka mana mu “yi tsaro” kuma mu yi shiri don ranar Jehobah? Muna bukatar mu ƙuduri niyyar yin abin da ya dace. Amma akwai wasu abubuwan da za mu ƙara yi. ’Yan kwanaki kafin abin da ya faru a lambun Jathsaimani, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su roƙi Jehobah ya taimake su. (Karanta Luka 21:36.) Saboda haka, wajibi ne mu riƙa yin addu’a idan muna so mu kasance a faɗake.—1 Bit. 4:7.

KU CI GABA DA YIN TSARO

17. Ta yaya za mu tabbata cewa muna shirye don abin da zai faru a nan gaba?

17 Tun da Yesu ya ce ƙarshe zai zo a “sa’ar da ba [mu] sa tsammani ba,” yanzu ba lokaci ba ne da za mu yi sanyin gwiwa a bautarmu ga Jehobah, kuma ba lokacin biɗan abin duniya da sha’awoyin jiki ba ne. (Mat. 24:44) Ta hanyar Littafi Mai Tsarki, Allah da Yesu sun bayyana abin da za su yi mana a nan gaba da kuma yadda za mu kasance a faɗake. Muna bukatar mu mai da hankali ga ibadarmu da kuma dangantakarmu da Jehobah. Ƙari ga haka, mu riƙa biɗan Mulkin Allah farko a rayuwarmu. Wajibi ne mu tuna cewa muna gab da ƙarshen duniya kuma mu kasance a shirye don abubuwan da za su faru. (R. Yoh. 22:20) Ta yin hakan ne za mu tsira!

^ [1] (sakin layi na 14) Ka duba babi na 21 a cikin littafin nan Mulkin Allah Yana Sarauta!