Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Ka karanta dukan fitowar Hasumiyar Tsaro ta shekarar nan da kyau? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Me ake nufi da ‘sabunta tunaninmu da hankalinmu’? (Rom. 12:2)

Hakan ba ya nufin mu yi wasu ayyuka masu kyau kawai. A maimakon haka, dole ne mu bincika halayenmu kuma mu yi canje-canje da za su sa mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi ƙaꞌidodin Jehobah.—w23.01, shafuffuka na 8-9.

Ta yaya za mu kasance da raꞌayi da ya dace game da abubuwan da suke faruwa a duniya?

Muna lura da yadda abubuwan da suke faruwa suke cika annabci Littafi Mai Tsarki. Amma bai kamata mu soma cewa abin da shugabannin duniya suke faɗa yana cika annabcin da ke 1 Tasalonikawa 5:​3 ba, domin hakan zai iya jawo rashin haɗin kai a ikilisiya. A maimakon haka, zai dace mu mai da hankali ga bayanin da ƙungiyarmu ta yi a kan wannan batun. (1 Kor. 1:10)—w23.02, shafi na 16.

Ta yaya baftismar Yesu ta bambanta da na mabiyansa?

Yesu ba ya bukatar ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kamar yadda muka yi, domin an haife shi a alꞌummar da ta riga ta yi alkawarin bauta wa Jehobah. Ba ya bukatar ya tuba daga zunubi domin shi kamiltaccen mutum ne.—w23.03, shafi na 5.

Ta yaya za mu ba wa mutane damar yin kalami?

Idan muna yin gajerun kalamai, hakan zai ba wa ꞌyanꞌuwanmu damar yin kalami. Mu kuma guji yin magana a kan batutuwa da yawa. Hakan zai sa sauran ꞌyanꞌuwa su sami abin da za su faɗa.—w23.04, shafi na 23.

Mene ne “Hanyar Tsarki” da ke Ishaya 35:8 take nufi?

Da farko, hanyar tana nufin hanyar da Yahudawa suka bi daga Babila zuwa ƙasar Israꞌila. Amma mene ne hanyar take nufi a zamaninmu? Ɗarurruwan shekaru kafin 1919, an yi gyare-gyare da ake bukata a hanyar ta wajen fassara da kuma buga Littafi Mai Tsarki da ma wasu littattafai. Cikin salama da haɗin kai, bayin Jehobah sun yi shekaru da dama suna tafiya a “Hanyar Tsarki,” wadda za ta kai su aljanna inda za su mori albarku da yawa.—w23.05, shafuffuka na 15-19.

Waɗanne mata biyu ne Karin Magana sura 9 ta yi amfani da su don ta ba mu shawara?

Littafin Karin Magana ya yi magana game da macen da take wakiltar “wawanci,” wadda take gayyatar mutane zuwa ga mutuwa. Da kuma macen da take wakiltar “hikima,” wadda take gayyatar mutane zuwa ga “ganewa” da kuma rai. (K. Mag. 9:​1, 6, 13, 18)—w23.06, shafuffuka na 22-24.

Ta yaya yadda Jehobah ya bi da Lot ko kuma Lutu ya nuna cewa shi mai sauƙin kai ne da kuma sanin yakamata?

Jehobah ya umurci Lutu ya gudu daga Sodom ko kuma Saduma zuwa yankunan tuddai. Amma da Lutu ya roƙa cewa a bar shi ya gudu zuwa Zowar maimakon yankunan tuddan, Jehobah ya amince da hakan.—w23.07, shafi na 21.

Mene ne mace za ta yi idan maigidanta yana kallon batsa?

Ya kamata ta tuna cewa ba laifinta ba ne. Ta mai da hankali ga kyautata dangantakarta da Jehobah, kuma ta yi tunani a kan labaran mata a Littafi Mai Tsarki da Jehobah ya ƙarfafa su saꞌad da suke baƙin ciki. Za ta iya taimaka wa maigidanta ya guji yanayoyi da za su sa shi ya kalli batsa.—w23.08, shafuffuka na 14-17.

Idan wani ya zolaye mu saboda imaninmu, ta yaya fahimi zai taimaka mana mu amsa masa ba tare da fushi ba?

Za mu iya amfani da damar mu san raꞌayin mutumin ko kuma abin da yake da muhimmanci a gare shi. Sanin hakan zai taimaka mana mu mai da martani ba tare da yin fushi ba.—w23.09, shafi na 17.

Ta yaya misalin Maryamu ya koya mana yadda za mu iya samun ƙarfafa?

Da zarar Maryamu ta ji cewa ita ce za ta zama mamar Almasihu, ta nemi ƙarfafa daga wurin wasu. Malaꞌika Jibraꞌilu da Alisabatu sun yi amfani da Nassosi sun ƙarfafa Maryamu. Mu ma za mu iya samun ƙarfafa daga ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci.—w23.10, shafi na 15.

A waɗanne hanyoyi ne Jehobah zai iya amsa adduꞌoꞌinmu?

Ya yi alkawarin cewa zai ji adduꞌoꞌinmu kuma zai duba ko sun jitu da nufinsa. (Irm. 29:12) Zai iya amsa adduꞌoꞌi iri ɗaya a hanyoyi dabam-dabam. Amma zai ci-gaba da taimaka mana.—w23.11, shafuffuka na 21-22.

Romawa 5:2 ta ambaci “sa zuciya,” to me ya sa aka sake yin zancenta a aya ta 4?

Bayan mutum ya ji albishiri daga Kalmar Allah, zai iya sa zuciya ga yin rayuwa a aljanna. Amma idan ya fuskanci matsaloli, ya jimre matsalolin kuma ya ga tabbacin cewa Allah ya yarda da shi, zai ƙara sa zuciya ko yin bege, kuma zai gaskanta cewa shi ma zai sami ladan nan.—w23.12, shafuffuka na 12-13.