Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 19

WAƘA TA 22 Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?

Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?

“Ubangiji . . . ba ya so wani ya halaka.”2 BIT. 3:9.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga tabbaci cewa saꞌad da Jehobah zai yi wa mutane shariꞌa a nan gaba, zai yi adalci.

1. Me ya nuna cewa muna rayuwa ne a lokaci mai muhimmanci?

 MUNA rayuwa ne a lokacin da abubuwa masu muhimmanci suke faruwa! Kowace rana, muna ganin cikar annabcin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, muna ganin yadda “sarkin arewa” da “sarkin kudu” suke jayayya da juna domin kowannensu yana ƙoƙarin samun ƙarfin faɗa a ji a duniya. (Dan. 11:40) Muna kuma ganin yadda ake waꞌazi a dukan duniya, kuma miliyoyin mutane sun zaɓi su bauta ma Jehobah. (Isha. 60:22; Mat. 24:14) Ƙari ga haka, muna samun abubuwa da yawa da za su taimaka mana mu ƙarfafa dagantakarmu da Jehobah “a kan lokaci.”—Mat. 24:​45-47.

2. Wane tabbaci ne muke da shi, amma me ya kamata mu tuna?

2 Jehobah ya ci-gaba da ba mu ƙarin haske a kan abubuwa masu muhimmanci da za su faru a nan gaba. (K. Mag. 4:18; Dan. 2:28) Ba shakka, kafin a soma ƙunci mai girma, Jehobah zai bayyana mana kome da kome da muke bukatar mu sani don mu iya riƙe amincinmu, kuma mu bauta masa da haɗin kai a lokacin. Amma mu tuna cewa a yanzu, akwai abubuwan da ba mu sani ba game da nan gaba. A wannan talifin, za mu ga abin da ya sa muka canja bayanin da muka yi a dā a kan wasu abubuwa da za su faru a nan gaba. Bayan haka, za mu tattauna wasu abubuwa da muka sani game da abin da zai faru da matakin da Ubanmu na sama zai ɗauka.

ABIN DA BA MU SANI BA

3. A dā me muka ce game da lokacin da Jehobah zai rufe ƙofar samun ceto, kuma me ya sa muka ce hakan?

3 A dā mun ce da zarar an soma ƙunci mai girma, mutane ba za su iya soma bauta ma Jehobah kuma su tsira ma yaƙin Armageddon ba. Mun faɗi hakan ne domin mun zata kowane abin da ya faru a zamanin Nuhu, alama ne na abin da zai faru a zamaninmu. Alal misali, mun ɗauka cewa kamar yadda Jehobah ya rufe ƙofar jirgin kafin a soma ambaliyar ruwan, haka ma, da zarar an soma ƙunci mai girma, Jehobah zai rufe ƙofar samun ceto. Wato, duk wanda ba ya bauta masa, ba zai iya samun ceto kuma ba.—Mat. 24:​37-39.

4. Shin yanzu muna ɗaukan dukan abubuwan da suka faru a zamanin Nuhu a matsayin alamu na abubuwan da za su faru a nan gaba? Ka bayyana.

4 Ya dace mu ce dukan abubuwan da suka faru a zamanin Nuhu alamu ne na abubuwan da za su faru a nan gaba? Aꞌa. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki bai faɗi hakan ba. a Yesu ya kwatanta abin da zai faru a lokacin da zai bayyana da abin da ya faru “a kwanakin Nuhu.” Amma bai ce duk wani abin da ya faru a lokacin Nuhu, yana nufin wani abin da zai faru a nan gaba ba. Alal misali, bai ce yadda Jehobah ya rufe ƙofar jirgin yana da wata maꞌana ba. Duk da haka, za mu iya koyan darussa daga abin da ya faru a zamanin Nuhu.

5. (a) Wane mataki ne Nuhu ya ɗauka kafin a soma ambaliyar ruwa? (Ibraniyawa 11:7; 1 Bitrus 3:20) (b) Wane alaƙa ne ke tsakanin waꞌazin da Nuhu ya yi da wanda muke yi a yau?

5 Da Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa zai halaka duniya da ruwa, Nuhu ya nuna bangaskiyarsa ta wurin gina jirgi. (Karanta Ibraniyawa 11:7; 1 Bitrus 3:20.) A yau ma, waɗanda suke jin bisharar Mulkin Allah da muke yi suna bukatar su ɗauki mataki. (A. M. 3:​17-20) Manzo Bitrus ya ce Nuhu “mai waꞌazin adalci” ne. (2 Bit. 2:5) Amma, kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, ko da yake Nuhu ya yi iya ƙoƙarinsa ya yi waꞌazi, Littafi Mai Tsarki bai gaya mana cewa ya yi wa kowa a duniya waꞌazi kafin a soma ambaliyar ruwan ba. A yau muna ƙoƙarin yi wa kowa a duniya waꞌazi kuma muna hakan da ƙwazo sosai. Amma duk ƙoƙarinmu, ba za mu iya yi wa kowa da kowa waꞌazi kafin ƙarshen duniyar nan ya zo ba. Me ya sa muka ce hakan?

6-7. Me ya nuna cewa ba zai yiwu mu yi wa kowa da kowa a duniya waꞌazi kafin ƙarshen ya zo ba? Ka bayyana.

6 Ka lura da abin da Yesu ya ce game da waꞌazin da muke yi. Ya ce za a ba da wannan labari mai daɗi “domin shaida ga dukan alꞌumma.” (Mat. 24:14) Ba a taɓa cika wannan annabcin kamar yadda ake cika shi a yau ba. Ana waꞌazin Mulkin Allah a yaruka fiye da 1,000 kuma an tanadar da wannan saƙon a dandalin jw.org don yawancin mutane a duniya su iya samunsa cikin sauƙi.

7 Amma Yesu ya kuma gaya wa almajiransa cewa, ‘kafin su gama zagaya dukan garuruwan,’ wato kafin su yi ma kowa-da-kowa waꞌazi, zai dawo. (Mat. 10:23; 25:​31-33) Hakan yana nufin cewa kafin mu yi wa kowa-da-kowa waꞌazi, Yesu zai dawo ya yi wa mutane shariꞌa. Domin miliyoyin mutane a yau suna zama a wuraren da ba a barin mu mu yi waꞌazi a sake. Ƙari ga haka, kowane minti ana haifan ɗarurruwan yara. Muna iya ƙoƙarinmu mu yi wa “kowace alꞌumma, da zuriya, da yare, da kabila” waꞌazi. (R. Yar. 14:6) Amma a gaskiya, ba za mu iya yi wa kowa da kowa waꞌazi kafin ƙarshen duniyar nan ya zo ba.

8. Wace tambaya ce za mu iya yi game da shariꞌar da Jehobah zai yi a nan gaba? (Ka kuma duba hotunan.)

8 Hakan ya ta da wata tambaya kuma, wato: Me zai faru da waɗanda ba su samu damar jin waꞌazinmu ba kafin a soma ƙunci mai girma? Wane mataki ne Jehobah da Ɗansa, wanda Jehobah ya ba wa aikin yin shariꞌa, za su ɗauka a kansu? (Yoh. 5:​19, 22, 27; A. M. 17:31) Nassin da muke tattaunawa a wannan talifin ya ce, Jehobah “ba ya so wani ya halaka.” A maimako, yana so “kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9; 1 Tim. 2:4) Don haka, gaskiyar ita ce Jehobah bai gaya mana matakin da zai ɗauka a kan waɗannan mutane ba. Kuma, ba dole ba ne ya gaya mana.

Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka a kan waɗanda ba su samu damar jin waꞌazin Mulkinsa kafin a soma ƙunci mai girma ba? (Ka duba sakin layi na 8) c


9. Mene ne Jehobah ya bayyana mana a Littafi Mai Tsarki?

9 A Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya bayyana mana wasu abubuwan da zai yi. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah zai ta da “marasa adalci” da ba su sami damar jin waꞌazin Mulkin Allah da yin tuba ba. (A. M. 24:15; Luk. 23:​42, 43) Amma hakan ya sake ta da wasu tambayoyi.

10. Waɗanne tambayoyi ne kuma suka taso?

10 Me zai faru da dukan waɗanda za su mutu a lokacin ƙunci mai girma? Za su halaka ke nan har abada? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah da rundunarsa za su halaka maƙiyansa a yaƙin Armageddon, kuma ba za a ta da mutanen nan ba. (2 Tas. 1:​6-10) Amma sauran mutanen fa? Alal misali, a lokacin ƙunci mai girma, mai yiwuwa wasu su mutu saboda rashin lafiya ko tsufa ko wani hatsari ko don wasu mutane sun kashe su. (M. Wa. 9:11; Zak. 14:13) Shin za a ta da mutanen nan lokacin da za a ta da “marasa adalci” a sabuwar duniya? Ba mu sani ba.

ABIN DA MUKA SANI

11. Bisa ga mene ne Jehobah zai shariꞌanta mutane?

11 Akwai abubuwa da yawa da muka sani game da nan gaba. Alal misali, mun san cewa za a shariꞌanta mutane ne bisa ga abubuwan da suka yi wa ꞌyanꞌuwan Yesu. (Mat. 25:40) Waɗanda suka goyi bayan shafaffun Kiristoci da kuma Yesu Kristi ne za a ce da su tumaki. Mun san cewa wasu ꞌyanꞌuwan Yesu za su kasance a duniya bayan an soma ƙunci mai girma, kuma ba za a ɗauke su zuwa sama ba sai dab da lokacin da za a soma yaƙin Armageddon. Da yake ꞌyanꞌuwan Yesu za su kasance a duniya, mai yiwuwa wasu mutane masu zuciyar kirki su samu damar goyon bayan shafaffun Kiristoci da kuma aikin da za su yi a wannan lokacin. (Mat. 25:​31, 32; R. Yar. 12:17) Me ya sa sanin hakan yake da muhimmanci?

12-13. Mene ne wataƙila wasu mutane za su yi, idan suka ga cewa an halaka Babila Babba? (Ka kuma duba hotunan.)

12 A lokacin ƙunci mai girma, idan wasu suka ga yadda aka halaka “Babila Mai Girma” wato Babila Babba, wataƙila su tuna cewa Shaidun Jehobah sun daɗe suna cewa hakan zai faru. Wa ya san ko wasu daga cikinsu za su soma bauta wa Jehobah?—R. Yar. 17:5; Ezek. 33:33.

13 Irin abin da ya faru ke nan a ƙasar Masar a zamanin Musa. Ka tuna cewa “Mutane masu yawa waɗanda” ba Israꞌilawa ba sun bi Israꞌilawan, kuma sun fita daga ƙasar Masar. (Fit. 12:38) Wataƙila wasunsu ba su ba da gaskiya ba, sai da suka ga Annoba Goma da Musa ya ce za su sauko musu sun faru da gaske. Idan wasu suka soma bauta ma Jehobah bayan an halaka Babila Babba, za mu yi fushi cewa Jehobah ya bar wasu su samu ceto dab da yaƙin Armageddon? Aꞌa. Ba za mu yi hakan ba! Zai dace mu bi halin Ubanmu na sama, “Allah mai jinƙai, . . . mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma.” bFit. 34:6.

Idan wasu suka ga halakar Babila Babba wataƙila su tuna cewa Shaidun Jehobah sun daɗe suna cewa hakan zai faru (Ka duba sakin layi na 12-13) d


14-15. Shin, lokacin da mutum ya mutu ko kuma inda yake zama ne zai sa ya samu rai na har abada ko ya rasa shi? Ka bayyana. (Zabura 33:​4, 5)

14 Wani zai iya ce, “Gwamma da dangina da ba Mashaidi ba ya rasu kafin a soma ƙunci mai girma, domin hakan zai sa a ta da shi.” Ƙauna ce take sa mutum ya faɗi haka. Amma fa, ba lokacin da mutum ya mutu ne zai sa a ta da shi, ko a ƙi ta da shi ba. Jehobah Alƙali ne nagari kuma a koyaushe yakan yi shariꞌar da ta dace. (Karanta Zabura 33:​4, 5.) Ba shakka, ‘Mai Shariꞌar dukan duniya’ zai yi adalci.—Far. 18:25.

15 Ƙari ga haka, ba inda mutum yake zama ne zai sa ya samu rai na har abada ko ya rasa ba. Akwai miliyoyin mutanen da ba su taɓa jin waꞌazin Mulkin Allah ba, domin yanayin ƙasashen da suke zama. Ba zai dace mu ce Jehobah zai shariꞌanta mutanen nan a matsayin “awaki” ba. (Mat. 25:46) Allahnmu mai yin shariꞌar gaskiya, ya ma fi mu damuwa a kan waɗannan mutanen. Ba mu san yadda Jehobah zai yi abubuwa a lokacin ƙunci mai girma ba. Wataƙila wasu mutanen nan za su soma bauta ma Jehobah idan suka ga yadda ya ɗaukaka sunansa a dukan duniya a lokacin ƙunci mai girma.—Ezek. 38:16.

Idan wasu suka ga yadda aka halaka Babila Babba . . . wa ya san ko wasu daga cikinsu za su bauta wa Jehobah?

16. Mene ne nazarin Littafi Mai Tsarki ya koya mana game da Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

16 Nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa mun ga cewa Jehobah yana ɗaukan ran mutum da daraja sosai. Ya ba da Ɗansa don dukanmu mu samu damar yin rayuwa har abada. (Yoh. 3:16) Dukanmu za mu yarda cewa Jehobah ya nuna mana ƙauna da tausayi. (Isha. 49:15) Jehobah ya san sunan kowannenmu. Ya san mu sosai, shi ya sa ko mun mutu zai iya ta da mu daidai yadda muke kafin mu mutu. (Mat. 10:​29-31) Hakika, akwai dalilai da yawa da suka tabbatar mana da cewa Ubanmu na sama mai ƙauna, zai yi wa kowa shariꞌar gaskiya domin shi mai hikima ne, mai adalci ne da kuma jinƙai.—Yak. 2:13.

Muna da tabbaci cewa Jehobah zai yi wa kowa shariꞌar gaskiya domin shi mai hikima ne, mai adalci ne, da kuma jinƙai (Ka duba sakin layi na 16)


17. Me za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Wannan ƙarin hasken da muka samu ya nuna cewa muna bukatar mu yi waꞌazi da gaggawa sosai. Me ya sa muka ce hakan? Kuma me zai sa mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo? Za mu tattauna amsoshin tambayoyin nan dalla-dalla a talifi na gaba.

WAƘA TA 76 Yin Waꞌazi Yana Sa Mu Murna

a Don ka fahimci abin da ya sa aka yi wannan canjin, ka karanta talifin nan, “Haka Nan Ya Gamshe Ka Sarai” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2015, Shafuffuka na 7-11.

b Bayan an halaka Babila Babba, za a jarraba dukan bayin Allah a lokacin da Gog na ƙasar Magog zai kawo mana hari. Za a jarraba duk wani mutumin da ya soma bauta ma Jehobah tare da mutanensa bayan halakar Babila Babba.

c BAYANI A KAN HOTUNA: Hotunan sun nuna abubuwa uku da za su iya hana wasu jin waꞌazin da muke yi a dukan duniya: (1) Wata mata tana zama a inda addinin da aka fi bi a wurin ba addinin Kirista ba ne, kuma yin waꞌazi a wurin yana da haɗari sosai, (2) wani mutum da matarsa suna zama a inda gwamnatin wurin ta hana aikinmu, kuma tana tsananta mana, kuma (3) wani mutum yana zama a wani daji da ba za mu iya zuwa ba.

d BAYANI A KAN HOTO: Wata da ta daina bauta ma Jehobah a dā, ta tuna abin da ta koya game da halakar Babila Babba, sai ta tuba kuma ta koma wurin iyayenta da suke bauta ma Jehobah. Idan abu kamar haka ya faru zai dace mu zama masu jinƙai da tausayi kamar Ubanmu na sama, kuma mu yi farin ciki cewa wani ya komo gare shi.