Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ʼYar Kirki

ʼYar Kirki

Ka saukar:

  1. 1. Ya ga haihuwarta,

    Da girman ta.

    ʼYar za ta fuskanci,

    Matsaloli fa.

    Amma idan ta yi

    Iya kokari,

    Tana sa shi yin murna.

    (AMSHI)

    ʼYa mai kirki, Yana kaunarki.

    Zai ci gaba da kaunarki.

  2. 2. Tana son yin kwazo—

    A aikinta.

    Shawarar babanta

    Na taimake ta,

    Kuma tana murna

    Don yana sonta.

    Tana murna idan ya ce:

    (AMSHI)

    “ʼYa mai kirki, Ina kaunarki.

    Zan ci gaba da kaunarki.”

    (KAFIN AMSHI)

    Allah na gani

    Kuma ya sani

    Duk kokarinki

    Da duk kaunarki.

    Jehobah Allah

    Ba zai manta da

    ʼYar kirki ba.

    (AMSHI)

    ʼYa mai kirki, Yana kaunarki.

    ʼYa mai kirki, Zai taimake ki.

    ʼYa mai kirki, Zai kula da ke.

    ʼYa mai kirki, Mai kima.