Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Neman Gaskiya

Neman Gaskiya

Ka Saukar:

  1. 1. In ‘kun nema, za ku samu’

    Abin da muka ji, ke nan.

    Akwai abubuwa, da muke so mu

    San game da Allahnmu.

    (KAFIN AMSHI)

    Kamar mai neman, zinariya fa,

    Ba za mu gaji ba, mun san akwai gaskiyar.

    (AMSHI)

    Muna neman amsa ga

    Duk tambayoyinmu,

    Da ba mu fahimce su ba:

    Game da rayuwa, da abin da ya sa Mulkin Allah zai zo.

    Za mu ta nema.

  2. 2. Ba mu san da sunan Allah ba,

    Jehobah shi ne sunan Allah.

    Ta hakan mun, soma samun

    Abin da muke nema.

    (KAFIN AMSHI)

    Mun ci gaba da, neman amsoshi,

    Game da Allah da rayuwarmu a, nan gaba.

    (AMSHI)

    Muna neman amsa ga

    Duk tambayoyinmu,

    Da ba mu fahimce su ba:

    Game da rayuwa, da aljanna da Allah ya yi alkawarin sa.

    Za mu san amsar.

    (KAFIN AMSHI)

    Yanzu mun shirya mu je, mu gaya ma wasu

    Abin da muka koya,

    Muna so mu, taimaka musu don

    Su ma su, san Allahnmu,

    Mu koya musu Kalmarsa.

    (AMSHI)

    Suna neman amsa ga

    Duk tambayoyinsu,

    Da ba su fahimce su ba:

    Game da duniya, da rayuwa har abada a aljanna

    Za ka san amsar.