Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Dauka Muna Aljanna

Ka Dauka Muna Aljanna

Ka Saukar:

  1. 1. Rayuwa akwai wahala.

    Abinci na wuyar samu.

    Amma ina yin tunani

    A kan bege na nan gaba.

    (AMSHI)

    Ka dauka muna cikin Aljanna,

    Sai jin dadi, ba za mu tsufa ba.

    Kullum za mu farka mu ce wa Allah,

    “Muna mika ma godiya don rayuwar nan!”

  2. 2. Kunnuwana ba su jin kome.

    Ba na ganin wuri sosai.

    A nan gaba zan soma ji.

    Idanuna za su bude.

    (AMSHI)

    Ka dauka muna cikin Aljanna,

    Sai jin dadi, ba za mu tsufa ba.

    Kullum za mu farka mu ce wa Allah,

    “Muna mika ma godiya don rayuwar nan!”

    (KAFIN AMSHI)

    Ko da ba na iya yin tafiya.

    A Aljanna, har gudu zan yi!

    (AMSHI)

    Ka dauka muna cikin Aljanna

    Sai jin dadi, ba za mu tsufa ba.

    Murna kawai za mu rika yi koyaushe!

    Jin dadi zai yi ta karuwa.

    (AMSHI)

    Ka dauka muna cikin Aljanna,

    Sai jin dadi, ba za mu tsufa ba.

    Kullum za mu farka mu ce wa Allah,

    “Muna mika maka godiya!”