Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Rayuwa a Cikin Aljanna

Rayuwa a Cikin Aljanna

Ka Saukar:

  1. 1. Ka zauna ka yi tunani cewa

    Kana rayuwa a cikin aljanna

    Yara suna wasa

    Ba tashin hankali ko rigima

    Mutanen da suke kaunar Allah

    Su ne suke kula da duniyar nan:

    ‘Muddin wata na nan’​—⁠

    Za mu zauna lafiya da kowa.

    Za mu ga kaunar

    Allah da kuma Dansa

    A cikin aljanna.

    (AMSHI)

    Bege na karfafa mu.

    Yana sa mu rike aminci.

    Kamar rana, yana haskawa

    Idan mun ga kanmu

    A cikin aljanna.

  2. 2. Ka rufe ido ka yi tunani

    Cewa ka gina gida a bakin rafi

    Ko a kan duwatsu.

    Sai ga wani da ka waye shi,

    Yana zuwa gidanka,

    Kun gudu kun rike junanku,

    Kuma kuna murna,

    Domin ya dade da kuka ga juna.

    Ko mutuwa ma

    Ba ta da iko

    A cikin aljanna.

    (AMSHI)

    Bege na karfafa mu.

    Yana sa mu rike aminci.

    Kamar rana, yana haskawa

    Idan mun ga kanmu

    A cikin aljanna.

    3. Zai cika duk nufinsa

    Za su faru fa, yadda ya ce.

    Jehobah zai tabbata, ya

    Cika dukan muradin ’yan Adam.

    (AMSHI)

    Bege na karfafa mu.

    Yana sa mu rike aminci.

    Kamar rana, yana haskawa

    Idan mun ga kanmu

    A cikin aljanna.

    A cikin aljanna,

    A cikin aljanna,

    A cikin aljanna.