Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Rabin Raina

Rabin Raina

Ka Saukar:

  1. 1. Ke kaɗai,

    Ce abin ƙaunata.

    Mai so na,

    Da nake ƙauna.

    Halayenki duka​—

    Suna sa ni murna.

    Da ni da ke,

    Za mu yi rayuwa.

    Kin kasance da ni

    Kina taimaka min.

    Na san cewa kina;

    Alfahari da ni.

    (AMSHI)

    Za mu kasance tare;

    Za mu more rayuwa.

    Jehobah zai taimaka mana kullum​—

    Rabin raina.

  2. 2. Kai nake ƙauna;

    Kana jin kukata.

    Kuma tare,

    Muke ibadarmu.

    Na san cewa kana

    Ƙauna ta a kullum.

    Har abada zan yi​—

    Alfahari da kai/ke.

    (AMSHI)

    Za mu kasance tare;

    Za mu more rayuwa.

    Jehobah zai taimaka mana kullum​—

    Rabin raina.

    Za mu kasance tare;

    Za mu more rayuwa.

    Jehobah zai taimaka mana kullum​—

    Rabin raina,

    Ina son ki,

    Sosai.