Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kiyaye Zuciyarka

Ka Kiyaye Zuciyarka

Ka Saukar:

  1. 1. Ina son yin abu mai kyau,

    Amma nakan damu sosai.

    Abin ya fi karfina,

    Ba zan iya hakan ba.

    Ina ma addu’a kullum

    Domin ka ce in rika yin hakan.

    A lokacin damuwa,

    Jehobah, Uba ka ce min,

    (AMSHI)

    In rika kiyaye zuciyata,

    In rika yin farin ciki.

    Zan ci gaba da yin nufinka.

    Zan yi hankali da zuciyata.

  2. 2. Ina son in yi nufinka,

    Amma ina sanyin gwiwa,

    Rayuwar nan ba sauki,

    Abin da wuya sosai.

    Duk da haka ina fita

    Don in yi wa mutane wa’azi.

    Ba zan daina hakan ba.

    Jehobah, Uba, kana nan.

    (AMSHI)

    Zan rika kiyaye zuciyata,

    Zan rika yin farin ciki.

    Zan ci gaba da yin nufinka.

    Zan yi hankali da zuciyata.

    Zuciyata.

  3. 3.

    Zan daina tunanin abin

    Da ke sa ni bakin ciki,

    Ina ganin cewa na kasa.

    Jehobah, na san kana tare da ni.

    Kana tare da ni.

    (AMSHI)

    Zan rika kiyaye zuciyata,

    Zan rika yin farin ciki.

    Zan ci gaba da yin nufinka.

    Zan yi hankali da zuciyata.