Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mu Zama da Bangaskiya

Mu Zama da Bangaskiya

(Zabura 27:⁠13)

Ka Saukar:

  1. 1. Ba na tsoron zakuna.

    Ba na tsoron masifa.

    Don Jehobah Allahna,

    Yana tare da ni.

    Ba zan taba jin tsoro ba.

    (AMSHI)

    Da bangaski’a, na san zan sami ceto.

    Da bangaski’a, ba zan ji tsoro ba.

    Ba zan ja da baya ba

    Don Allah yana nan,

    Yana tare da ni koyaushe.

    Da bangaski’a.

  2. 2. Amintattun Jehobah

    Wadanda suka mutu

    Don bangaskiyarsu

    Allah zai ta da su.

    Kowa da kowa zai gan su.

    (AMSHI)

    Da bangaski’a, na san zan sami ceto.

    Da bangaski’a, ba zan ji tsoro ba.

    Ba zan ja da baya ba

    Don Allah yana nan,

    Yana tare da ni koyaushe.

    Da bangaski’a.

  3. 3.

    Da bangaski’a, zan iya ta da tuddai.

    Da bangaski’a, ni zan jimre.

    Bangaskiya

    Ce take taimaka mini

    In jimre da farin ciki.

  4. 4. Allah zai shirya mana,

    Aljanna a duni’a.

    A lokacin nan,

    Zai hallaka Shaidan,

    Da kuma dukan makiyansa.

    (AMSHI)

    Da bangaski’a, na san zan sami ceto.

    Da bangaski’a, ba zan ji tsoro ba.

    Ba zan ja da baya ba

    Don Allah yana nan,

    Yana tare da ni koyaushe.

    Da bangaski’a,

    Da bangaski’a.

(Ka kuma duba Ibran. 11:​1-40.)