Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Komo Gun Jehobah

Ka Komo Gun Jehobah

Ka Saukar:

  1. 1. A cikin duniyar nan,

    Don mu ajizai ne

    Ba wanda zai ce,

    “Ban taba yin kuskure ba.”

    Amma ka san cewa

    Idan ka yi kuskure,

    Za ka iya yin gyara.

    Ka komo ga Jehobah, Ubanmu.

    (AMSHI)

    Ka komo wurinsa.

    Ka yi kokarinka.

    Ka komo wurinsa.

    Ka bi umurninsa.

    Ka amince da shi.

    Yana kaunar ka sosai.

    Zai taimaka maka

    Ka zama amininsa

    Idan ka yi gyara.

  2. 2. Kullum, dare da rana,

    Kana cikin damuwa.

    Ka rasa me za ka yi.

    Ka sake tunani.

    In ka yi addu’a

    Ga Allahnmu Jehobah,

    Jehobah za ya ji ka.

    Da Kalmarsa zai taimaka maka.

    (AMSHI)

    Ka komo wurinsa.

    Ka yi kokarinka.

    Ka komo wurinsa.

    Ka bi umurninsa.

    Ka amince da shi.

    Yana kaunar ka sosai.

    Zai taimaka maka

    Ka zama amininsa.

  3. 3. Shawarar da ke Kalmarsa

    Za ta iya taimake ka.

    ‘Allah ya fi zuciyarka.’

    Ka gaskata!

    Zo gare shi.

    (AMSHI)

    Ka komo wurinsa.

    Ka yi kokarinka.

    Ka komo wurinsa.

    Ka bi umurninsa.

    Ka amince da shi.

    Yana kaunar ka sosai.

    Zai taimaka maka

    Ka zama amininsa,

    Idan ka yi gyara;

    Ka komo gun Allah.