Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Anini Biyu”

“Anini Biyu”

Ka Saukar:

  1. 1. Zuciyata

    Tana ta bugawa.

    Kudina

    Ba shi da yawa kamar na sauran.

    Ya Allahna,

    Aninai biyu ne nan.

    Na san za ka karba,

    Ko da yake ba shi da yawa.

    (AMSHI)

    Ko da kadan ne

    Jehobah yana so,

    Domin Ya san kokarinmu.

    Na san hakan domin

    Yana son mu sosai.

    Zai karbi gudummawata,

    Ba shakka!

  2. 2. A zucinta

    Kila ta manta cewa

    Takan bayar da

    Fiye da hakan idan ta samu.

    Da ta saka su

    Ba wanda ya ji karar.

    Amma ga Allahnmu,

    Wannan kyautar babban abu ne.

    (AMSHI)

    Ko da kadan ne

    Jehobah yana so,

    Domin Ya san kokarinmu.

    Na san hakan domin

    Yana son mu sosai.

    Zai karbi gudummawata,

    Ba shakka!

    3. Yana daraja duk kokarinmu,

    Ko da ba shi da yawa, Ya sani.

    Ya san zuciyarmu.

    (AMSHI)

    Ko da kadan ne

    Jehobah yana so,

    Domin Ya san kokarinmu.

    Na san hakan domin

    Yana son mu sosai.

    Zai karbi gudummawata,

    Ba shakka!

    Don Jehobah ya san kome.