Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ba Zai Yi Latti Ba!” (Wakar Taron Yanki na 2023)

“Ba Zai Yi Latti Ba!” (Wakar Taron Yanki na 2023)

(Habakkuk 2:3)

Ka Saukar:

  1. 1. Dukan duniya na da kyau sosai,

    Ta nuna cewa kai mai hakuri ne.

    Alkawuranka ba sa canjawa,

    Za ka cika su, “ba zai yi latti ba.”

    (AMSHI)

    Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,

    Don mu shiga Aljanna.

    Madaukaki, Uba, ka kawo Mulkinka.

    Mun san zai zo, ba shakka,

    Ba zai fasa ba!

  2. 2. Muna marmarin ganin lokacin

    Da amintattu da ke kabarbura,

    Za su sami rai a duniyar nan.

    Mu jimre sosai don mu marabce su.

    (AMSHI)

    Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,

    Don mu shiga Aljanna.

    Madaukaki, Uba, ka kawo Mulkinka.

    Mun san zai zo, ba shakka,

    Ba zai fasa ba!

  3. 3. Kana tattara masu kaunar ka

    Don su bauta ma, su sami albarka.

    Muna waꞌazi da himma sosai.

    Yin hakan na sa mu yi kusa da kai.

    (AMSHI)

    Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,

    Don mu shiga Aljanna.

    Madaukaki, Uba, ka kawo Mulkinka.

    Mun san zai zo, ba shakka,

    Ba zai fasa ba!

    Uba, ka sa mu jimre!

(Ka kuma duba Kol. 1:11.)