Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 3

Namiji Da Ta Mace Na Farko

Namiji Da Ta Mace Na Farko

MENENE ya bambanta wannan da wancan hoton? Hakika, mutanen ne da suke wannan. Sune namiji da ta mace na farko. Wanene ya halicce su? Allah ne. Ka san sunansa? Sunansa Jehobah ne. Kuma sunan namiji da ta mace na farko shi ne Adamu da Hauwa’u.

Ga yadda Jehobah Allah ya halicci Adamu. Ya ɗebi turɓayar ƙasa kuma ya mulmula jikin mutum kamiltacce da turɓayar. Sai ya hura masa numfashi a hanci, sai Adamu ya rayu.

Jehobah Allah ya ba Adamu aiki. Ya gaya masa ya ba da suna ga dukan dabbobi. Sai Adamu ya daɗe yana lura da dabbobin domin ya zaɓa musu suna da ya dace. Sa’ad da Adamu yake ba wa dabbobin suna ya fara lura da wani abu. Ka san ko menene wannan abin?

Dukan dabbobin suna da matansu. Da akwai Giwa baba da giwa mama, da kuma zaki baba da zaki mama. Amma Adamu ba shi da mata. Saboda haka, Jehobah ya sa Adamu ya yi barci mai zurfi, sai ya ɗauki ƙashi ɗaya a haƙarƙarinsa. Jehobah ya yi amfani da wannan ƙashin ya yi mace, da ta zama matarsa.

Adamu ya yi murna ƙwarai! Ka yi tunani kuma yadda Hauwa’u za ta yi murna da aka saka ta cikin wannan kyakkyawan lambu domin ta zauna! A yanzu suna iya haifan ’ya’ya su zauna tare suna farin ciki.

Jehobah yana so Adamu da Hauwa’u su rayu har abada. Yana so su mai da dukan duniya ta zama kyakkyawa kamar lambun Adnin. Adamu da Hauwa’u sun yi farin ciki ƙwarai da suka yi tunanin wannan! Da za ka so ka saka hannu wajen mayar da duniya ta zama kyakkyawan lambu? Amma farin cikin Adamu da Hauwa’u bai daɗe ba. Barimu ga abin da ya sa.

Zabura 83:18; Farawa 1:26-31; 2:7-25.