Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 4

Abin Da Ya Sa Suka Yi Rashin Gidansu

Abin Da Ya Sa Suka Yi Rashin Gidansu

DUBI abin da ke faruwa a yanzu. An kori Adamu da Hauwa’u daga kyakkyawan gidansu na lambun Adnin. Ka san abin da ya sa?

Domin sun yi wani abu ne mummuna ƙwarai. Saboda haka Jehobah yake yi musu horo. Ka san mummunan abin da Adamu da Hauwa’u suka yi?

Sun yi wani abin da Allah ya gaya musu kada su yi. Allah ya ce musu su ci kowane ’ya’yan itace da suke so a cikin lambu. Amma ya ce musu kada su ci wani ’ya’yan itace, domin idan sun ci za su mutu. Ya keɓe wannan itace ga kansa. Kuma mun sani cewa ba daidai ba ne mu ɗauki abin wani, ko ba haka ba? To, sai me ya faru?

Wata rana sa’ad da Hauwa’u tana cikin lambun ita kaɗai, sai maciji ya yi mata magana. Ka yi tunanin wannan! Ya ce wa Hauwa’u ta ci ’ya’yan itacen da Allah ya hana su. Amma, sa’ad da Jehobah ya halicci maciji bai halicce sa da yin magana ba. Wannan yana nufi ne cewa wani ne ya sa macijin ya yi magana. Wanene kuma wannan?

Ba Adamu ba ne. Saboda haka zai kasance wani ne da Allah ya halitta da daɗewa kafin ya halicci duniya. Waɗannan mutane mala’iku ne, kuma ba za mu iya ganinsu ba. Wannan mala’ika ya zama mai fahariya. Sai ya fara tunanin cewa zai zama mai sarauta kamar Allah. Kuma ya so mutane su yi masa biyayya maimakon su yi wa Jehobah. Shi ne mala’ika da ya sa macijin ya yi magana.

Wannan mala’ikan ya yi wa Hauwa’u wayo. Sa’ad da ya ce mata za ta zama kamar Allah idan ta ci wannan ’ya’yan itace, ta yarda da abin da ya ce. Sai ta ci, Adamu ma ya ci. Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah rashin biyayya, abin da ya sa ke nan suka yi rashin kyakkyawan gidansu na lambu.

Amma wata rana Allah zai sake sa a mai da dukan duniya ta zama kyakkyawa kamar lambun Adnin. Daga baya za mu koyi yadda kai ma za ka saka hannu hakan ya kasance. Amma a yanzu, bari mu ga abin da ya faru da Adamu da Hauwa’u.

Farawa 2:16, 17; 3:1-13, 24; Ru’ya ta Yohanna 12:9.