Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 5

An Fara Rayuwa Mai Wuya

An Fara Rayuwa Mai Wuya

ADAMU da Hauwa’u sun sha wuya ƙwarai bayan da suka fita daga cikin lambun Adnin. Sai sun wahala wajen aiki suke samun abinci. Maimakon itatuwa kyawawa masu ’ya’ya, suka ga ƙayayuwa da sarƙaƙiya suka yi ta tsiro musu. Abin da ya faru ke nan sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi rashin biyayya ga Allah suka ɓata abokantakar su da shi.

Mafi muni ma, Adamu da Hauwa’u suka fara mutuwa. Ka tuna Allah ya yi musu gargaɗi cewa za su mutu idan suka ci wani ’ya’yan itace. Hakika, a ranar da suka ci suka fara mutuwa. Sun yi wauta ƙwarai da suka ƙi yi wa Allah biyayya!

Adamu da Hauwa’u sun haifi dukan ’ya’yansu ne bayan Allah ya kore su daga lambun Adnin. Wannan yana nufin cewa ’ya’yansu ma za su tsufa kuma su mutu.

Da a ce Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah biyayya, da rayuwa ta kasance da daɗi ga su da ’ya’yansu. Da za su zauna har abada cikin jin daɗi a duniya. Da babu wanda zai tsufa, ko ya yi ciwo, ko ya mutu.

Allah yana son mutane su dawwama cikin farin ciki, kuma ya yi alkawarin cewa wata rana hakan zai faru. Dukan duniya za ta yi kyau kuma dukan mutane za su kasance da koshin lafiya. Kuma dukan mutane da suke duniya za su zama abokan juna kuma abokan Allah.

Amma Hauwa’u ba abokiyar Allah ba ce kuma. Saboda haka sa’ad da ta haifi ’ya’yanta ta sha wuya ƙwarai. Ta sha naƙuda. Rashin biyayya ga Jehobah ya jawo mata baƙin ciki ƙwarai, ko ba haka ba ne?

Adamu da Hauwa’u sun haifi ’ya’ya maza da mata da yawa. Sa’ad da suka haifi ɗansu na fari, suka saka masa suna Kayinu. Suka saka wa na biyun suna Habila.Menene ya same su? Ka san abin da ya same su?

Farawa 3:16-23; 4:1, 2; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.