Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 8

Ƙattai A Duniya

Ƙattai A Duniya

A CE wani yana zuwa wurinka kuma domin tsawonsa, kansa yana taɓa kan ɗakin gidanku, me kake tsammani? Lalle wannan mutumin ƙato ne! Da akwai zamanin da ake da ƙattai haka a duniya. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa iyayensu mala’iku ne daga sama. Yaya hakan ya kasance?

Ka tuna, mugun mala’ikan nan Shaiɗan yana nan yana ƙulle-ƙulle. Yana ƙoƙarin ya sa mala’ikun Allah su zama miyagu. Sai wasu cikinsu suka saurari Shaiɗan. Sun bar aikin da Allah ya ba su su yi a samaniya. Suka sauko duniya suka ɗauki jiki irin na mutane domin kansu. Ka san abin da ya sa?

Littafi Mai Tsarki ya ce domin waɗannan ’ya’yan Allah sun ga mata kyawawa a duniya kuma suna so su zauna tare da su ne. Saboda haka, suka sauko duniya suka auri waɗannan mata. Littafi mai tsarki ya ce wannan ba daidai ba ne, domin Allah ya halicci mala’iku su zauna a sama ne.

Sa’ad da waɗannan mala’iku da matansu suka haifi ’ya’ya, waɗannan ’ya’yan sun bambanta. Da farko sa’ad da suke jarirai ba su bambanta ba. Amma sai suka ci gaba da girma suna girma, suna ƙarfi suna ƙara ƙarfi, har sai da suka zama ƙattai.

Waɗannan ƙattai mugaye ne. Kuma domin su ƙattai ne kuma suna da ƙarfi sosai, sai suka soma cin zalin mutane. Suka yi ƙoƙari su tilasta wa kowa ya zama mugu kamarsu.

Ahnuhu ya riga ya mutu, amma da akwai mutumin kirki guda a duniya. Wannan mutumin sunansa Nuhu ne. Ko da yaushe yana yin abin da Allah ya ce masa ya yi.

Wata rana Allah ya gaya wa Nuhu cewa lokaci ya yi da zai halaka dukan miyagun mutane. Amma Allah zai ceci Nuhu, da kuma iyalinsa da kuma dabbobi da yawa. Bari mu ga yadda Allah ya yi haka.

Farawa 6:1-8; Yahuda 6.