Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 2

Daga Tufana Zuwa Ceto Daga Ƙasar Masar

Daga Tufana Zuwa Ceto Daga Ƙasar Masar

Mutane takwas ne kawai suka tsira daga Tufana, amma da shigewar lokaci suka ƙaru suka zama dubbai masu yawa. Shekara 352 bayan Tufana, aka haifi Ibrahim. Mun ga yadda Allah ya cika alkawarinsa ta wurin ba wa Ibrahim ɗa mai suna Ishaku. Sa’an nan cikin ’ya’yan Ishaku biyu Allah ya zaɓi Yakubu.

Yakubu kuma yana da babbar iyali da ’ya’ya maza 12 da ’yan mata. ’Ya’yan Yakubu maza 10 suka ƙi jinin ƙaninsu Yusufu suka kuwa sayar da shi bauta zuwa ƙasar Masar. Daga baya Yusufu ya zama masarauci mai martaba a ƙasar Masar. Da aka yi lokacin yunwa, sai Yusufu ya gwada ’yan’uwansa ya ga ko sun sake halinsu. Daga ƙarshe, dukan iyalin Yusufu, Isra’ilawa suka ƙaura zuwa ƙasar Masar. Wannan ya faru bayan an haifi Ibrahim da shekara 290.

Isra’ilawa suka yi shekara 215 a ƙasar Masar. Bayan mutuwar Yusufu, sai suka zama bayi a nan. Da shigewar lokaci aka haifi Musa, Allah kuwa ya yi amfani da shi wajen ceton Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Duka duka Sashe na BIYU ya ba da tarihin abin da ya faru cikin shekaru 857.