Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 11

Bakan Gizo Na Farko

Bakan Gizo Na Farko

KA SAN abin da Nuhu ya fara yi sa’ad da shi da iyalinsa suka fito daga cikin jirgi? Ya yi hadaya ko kuma kyauta ga Allah. Ga shi yana yin haka a wannan hoton da ke ƙasa. Nuhu ya ba da kyautar wannan dabbobi ne ya yi wa Allah godiya domin ya ceci iyalinsa daga tufana.

Kana tsammanin Jehobah ya yi farin ciki kuwa da wannan kyauta? Hakika, ya yi farin ciki. Sai kuma ya yi wa Nuhu alkawarin cewa ba zai sake halaka duniya da tufana ba.

Ba da daɗewa ba ruwan duka ya bushe, Nuhu kuma da iyalinsa suka fara sabuwar rayuwa a duniya. Allah ya yi musu albarka kuma ya ce musu: ‘Za ku haifi ’ya’ya da yawa. Za ku kuma ƙaru har sai mutane sun cika dukan duniya.’

Amma daga baya, sa’ad da mutane suka ji game da wannan tufana mai girma, wataƙila su ji tsoro cewa tufana za ta sake faruwa kuma. Saboda haka, Allah ya ba da alama da za ta tuna wa mutane alkawarinsa cewa ba zai sake halaka dukan duniya da tufana ba. Ka san alamar da ya bayar domin ya tuna musu? Bakan gizo ne.

Sau da yawa ana ganin bakan gizo a sama idan rana ta fito bayan a gama ruwa. Bakan gizo yana da launi masu kyau. Ka taɓa ganin bakan gizo? Ka ga wannan wanda yake cikin hoto?

Ga abin da Allah ya ce: ‘Na yi alkawarin cewa dukan mutane da dabbobi ba za su sake halaka ba da tufana. Zan ba da bakan gizo nawa a sama. Kuma dukan sa’ad da bakan gizo ya fito zan gani kuma in tuna da alkawarina.’

Saboda haka, idan ka ga bakan gizo, me ya kamata ya tuna maka? Hakika, alkawarin Allah cewa ba zai sake halaka duniya ba da tufana.

Farawa 8:18-22; 9:9-17.