Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 12

Mutane Sun Gina Babbar Hasumiya

Mutane Sun Gina Babbar Hasumiya

BAYAN shekaru da yawa. ’Ya’yan Nuhu suka haifi ’ya’ya da yawa. Kuma ’ya’yansu ma suka girma suka haifi ’ya’ya. Ba da daɗewa ba mutane suka yi yawa a duniya.

Ɗaya daga cikin waɗannan mutane tattaɓa kunnen Nuhu ne mai suna Nimʹrod. Mugun mutum ne wanda yake farautar dabbobi da mutane. Nimʹrod kuma ya mai da kansa sarki yana sarauta bisa wasu mutane. Allah ba ya son Nimʹrod.

A wannan lokacin dukan mutane yare ɗaya suke yi. Nimʹrod yana son ya tara su duka wuri ɗaya domin ya yi sarauta a kansu. Ka san abin da ya yi? Ya gaya wa mutanen su gina birni da kuma babbar hasumiya. Ka gansu a hoto suna yin tubali.

Jehobah bai yi farin ciki ba da wannan ginin da suke yi. Allah yana so mutanen su bazu zuwa dukan faɗin duniya. Amma mutanen suka ce: ‘Ku zo! Bari mu gina birni da kuma hasumiya mai tsawo da kanta zai taɓa sama. Da haka za mu zama fitattu!’ Mutanen suna son daraja ga kansu ba ga Allah ba.

Saboda haka, Allah ya sa mutanen suka daina ginin hasumiyar. Ka san yadda ya yi haka? Farat ɗaya ya sa mutanen suka fara yare dabam dabam maimakon ɗaya kawai. Saboda haka, masu ginin ba sa fahimtar juna. Abin da ya sa ke nan aka kira birninsu Babel, ko kuma Babila, wato, “Rikicewa.”

Sai mutanen suka fara ƙaura daga Babel. Mutane masu yare iri ɗaya suka koma da zama a wasu ɓangarorin duniya.

Farawa 10:1, 8-10; 11:1-9.