Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 13

Ibrahim, Abokin Allah

Ibrahim, Abokin Allah

ƊAYA daga cikin wuraren da mutane suka koma da zama bayan ruwan Tufana ana kiransa Ur. Ur ta zama muhimmiyar birni mai kyawawan gidaje. Amma mutanen da suke wannan birnin suna bauta wa gumaka. Haka ma suka yi a Babel. Mutanen da suke Ur da kuma Babel ba su bi halin Nuhu ba da ɗansa Shem, waɗanda suka ci gaba da bauta wa Jehobah.

A ƙarshe, shekara 350 bayan tufana, Nuhu mai bangaskiya ya mutu. Shekara biyu bayan mutuwarsa aka haifi wannan mutumi da kake gani a wannan hoto. Mutum ne mai muhimmanci ga Allah. Sunansa Ibrahim. Yana tare da iyalinsa a wannan birnin Ur.

Wata rana Jehobah ya gaya wa Ibrahim: ‘Ka bar ƙasar Ur da kuma danginka, ka je ƙasar da zan nuna maka.’ Shin Ibrahim ya yi wa Allah biyayya kuwa ya bar jin daɗin da yake yi a ƙasar Ur? Hakika ya yi haka. Kuma domin Ibrahim a kullum yana yi wa Allah biyayya shi ya sa ya zama abokin Allah.

Wasu cikin iyalansa sun bi shi sa’ad da ya bar ƙasar Ur. Babansa Teʹrah ya bi shi. Haka ma ɗan wansa Lutu. Da kuma Saratu matar Ibrahim. Da shigewar lokaci suka sauka a wani gari da ake kira Haran, a nan Teʹrah ya mutu. Sun riga sun yi nisa da Ur.

Bayan ɗan lokaci Ibrahim da iyalinsa suka bar Haran suka isa wata ƙasa da ake kiranta Kan’ana. A nan Jehobah ya ce: ‘Wannan shi ne ƙasar da zan ba ’ya’yanka.’ Ibrahim ya koma da zama a Kan’ana yana zama cikin tanti.

Allah ya taimake shi, Ibrahim ya sami garken tumaki da kuma wasu dabbobi masu yawa da ɗarurruwan bayi. Amma shi da Saratu ba su da ko ɗa guda na kansu.

Sa’ad da Ibrahim yake da shekara 99 da haihuwa, Jehobah ya ce masa: ‘Na yi maka alkawarin cewa za ka zama uban al’ummai da yawa na mutane.’ Amma ta yaya hakan zai faru, tun da Ibrahim da Saratu sun riga sun tsufa sun wuce lokacin haihuwa?

Farawa 11:27-32; 12:1-7; 17:1-8, 15-17; 18:9-19.