Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 14

Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim

Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim

KANA ganin abin da Ibrahim yake yi a nan? Yana riƙe da wuƙa kuma kamar zai yanka ɗansa. Me ya sa zai yi irin wannan abu? Da farko, bari mu ga yadda Ibrahim da Saratu suka sami ɗansu.

Ka tuna cewa Allah ya yi musu alkawari cewa za su sami ɗa. Amma hakan kamar ba zai yiwu ba, domin Ibrahim da Saratu sun riga sun tsufa. Amma Ibrahim ya yi imani cewa Allah zai iya yin abin da kamar ma ba zai yiwu ba. To menene ya faru?

Bayan Allah ya yi wannan alkawari, shekara ɗaya ya wuce. Sa’ad da Ibrahim ya cika shekara ɗari da haihuwa Saratu kuma shekara 90, suka haifi ɗa mai suna Ishaku. Allah ya cika alkawarinsa!

Amma sa’ad da Ishaku ya girma, sai Jehobah ya gwada bangaskiyar Ibrahim. Ya yi kira: ‘Ibrahim!’ Sai Ibrahim ya amsa: ‘Na’am!’ Sai Allah ya ce masa: ‘Ka ɗauki ɗan, tilonka Ishaku, ka tafi bisa wani dutse da zan nuna maka. A can za ka kashe shi ka miƙa shi hadaya.’

Waɗannan kalmomi ba su yi wa Ibrahim daɗi ba, domin Ibrahim yana ƙaunar ɗansa ƙwarai. Amma ka tuna cewa Allah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa ’ya’yansa za su zauna a ƙasar Kan’ana. Yaya hakan zai faru idan Ishaku ya mutu? Ibrahim bai fahimci haka ba amma kuma ya yi wa Allah biyayya.

Sa’ad da ya isa kan dutsen, Ibrahim ya ɗaure Ishaku kuma ya ɗaura shi a kan bagade da ya gina. Sai ya zaro wuƙa zai kashe ɗansa. A wannan lokaci kuwa sai mala’ikan Allah ya yi kira: ‘Ibrahim, Ibrahim!’ Sai Ibrahim ya amsa: ‘Na’am!’

Allah ya ce: ‘Kada ka yi wa saurayin rauni ko kuma wani abu. Kuma yanzu na sani cewa ka ba da gaskiya a gare ni, domin ba ka hana mini ɗanka tilonka ba.’

Ibrahim ya nuna bangaskiya mai girma ga Allah! Ya gaskata cewa babu abin da zai gagari Jehobah, yana iya ta da Ishaku daga matattu. Amma ba nufin Allah ba ne Ibrahim ya kashe Ishaku. Saboda haka Allah ya sa rago ya maƙale cikin ƙaya, kuma ya ce wa Ibrahim ya yi hadaya da ragon maimakon ɗansa.

Farawa 21:1-7; 22:1-18.