Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 15

Matar Lutu Ta Dubi Baya

Matar Lutu Ta Dubi Baya

LUTU da iyalinsa suka zauna tare da Ibrahim a ƙasar Kan’ana. Wata rana Ibrahim ya ce wa Lutu: ‘Ka ga babu isashen wuri a nan domin dabbobinmu duka. Don Allah ka ga gara mu rabu. Idan ka bi nan, sai ni in bi can.’

Lutu ya dubi duka ƙasar. Ya ga gefe mai kyau na ƙasar wanda yake da ruwa da kuma ciyayi da yawa domin dabbobinsa. Wato Gunduman Urdun. Sai Lutu ya ƙaura tare da iyalinsa da dabbobinsa zuwa can. A ƙasar suka zauna a birnin Saduma.

Mutanen Saduma miyagu ne ƙwarai. Wannan ya ɓata wa Lutu rai ƙwarai, domin shi mutumin kirki ne. Ran Allah ma ya ɓaci. A ƙarshe sai Allah ya aiki mala’iku biyu su yi wa Lutu gargaɗi cewa zai halaka Saduma da kuma Gwamarata birnin da ke kusa da shi domin muguntarsu.

Mala’ikun suka gaya wa Lutu: ‘Maza! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka mata biyu ka fita daga nan!’ Amma Lutu da iyalinsa suna ɗan jinkiri, saboda haka mala’ikun suka kama hannunsu suka fitar da su daga cikin birnin. Sai ɗaya daga cikin mala’ikan ya ce: “Ku gudu don ranku! Kada ku dubi baya. Ku gudu zuwa duwatsu saboda kada ku mutu.’

Lutu da ’ya’yansa mata suka yi biyayya suka gudu daga Saduma. Ba su tsaya ba ko na ɗan lokaci, kuma ba su dubi baya ba. Amma matar Lutu ta yi rashin biyayya. Bayan sun yi ɗan nisa da Saduma, ta tsaya ta dubi baya. Sai matar Lutu ta zama umudin gishiri. Ka ganta a wannan hoton?

Za mu iya koyon darassi mai kyau daga wannan. Wannan ya nuna mana cewa Allah yana ceton waɗanda suka yi masa biyayya, amma waɗanda suka ƙi yi masa biyayya za su rasa ransu.

Farawa 13:5-13; 18:20-33; 19:1-29; Luka 17:28-32; 2 Bitrus 2:6-8.