Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 18

Yakubu Ya Tafi Haran

Yakubu Ya Tafi Haran

KA SAN waɗannan mutanen da Yakubu yake magana da su? Bayan ya yi kwanaki yana tafiya Yakubu ya sadu da su a bakin rijiya. Suna kiwon tumaki. Yakubu ya yi tambaya: ‘Daga ina ne ku ka fito?’

Suka ce daga: ‘Haran.’

‘Ko kun san Laban?’ Yakubu ya yi tambaya.

‘E mun san shi,’ suka amsa. ‘Ga ’yarsa Rahila ma nan tafe da tumaki.’ Ka ga Rahila tana zuwa daga nesa?

Da Yakubu ya ga Rahila da tumakin kawunsa Laban, sai ya je ya buɗe rijiya domin a ba tumaki ruwa. Sai Yakubu ya sumbaci Rahila kuma ya gaya mata ko shi wanene. Ta yi farin ciki ƙwarai, ta koma gida ta je ta gaya wa babanta Laban.

Laban ya yi farin ciki da Yakubu ya zauna tare da shi. Kuma sa’ad da Yakubu ya ce zai auri Rahila, Laban ya yi farin ciki. Amma, Yakubu ya yi aiki a gonarsa na shekara bakwai kafin a ba shi Rahila. Domin yana son Rahila sosai Yakubu ya yi aikin. Amma da lokacin aure ya zo ka san abin da ya faru?

Laban ya bai wa Yakubu ’yar farinsa Lai’atu maimakon Rahila. Sa’ad da Yakubu ya yarda ya sake aiki na shekara bakwai kuma, Laban ya ba shi Rahila ta zama matarsa. A wannan lokacin Allah ya ƙyale mutane su auri fiye da mace ɗaya. Amma yanzu, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, mace ɗaya mutum zai aura.

Farawa 29:1-30.