Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 20

Dinah Ta Shiga Masifu

Dinah Ta Shiga Masifu

KA GA waɗanda Dinah ta je ziyartarsu? Tana zuwa ziyartar ’yan matan ƙasar Kan’ana. Babanta Yakubu zai ji daɗin wannan kuwa? Domin mu amsa wannan tambayar, ka tuna cewa Ibrahim da Ishaku ba sa son matan ƙasar Kan’ana.

Ibrahim yana son ɗansa Ishaku ya auri yarinya ’yar ƙasar Kan’ana ne? A’a, ba ya so. Ishaku da Rifkatu suna so ɗansu Yakubu ya auri yarinya daga ƙasar Kan’ana ne? A’a, ba su so ba. Ka san abin da ya sa?

Abin da ya sa shi ne mutanen Kan’ana allolin ƙarya suke yi wa bauta. Ba mutanen kirki ba ne da mutum zai aura, kuma ba mutanen kirki ba ne da mutum zai yi abokantaka da su. Saboda haka mun tabbata cewa Yakubu ba zai yi farin ciki ba cewa ’yarsa tana abota da ’yan matan ƙasar Kan’ana.

Kuma babu shakka, Dinah ta shiga masifa. Ka ga wannan mutumin Kan’ana da yake kalon Dinah a wannan hoto? Sunansa Shechem. Wata rana da Dinah ta zo wurinsu ziyara, She’chem ya nuna wa Dinah ƙarfi ya kwana da ita. Wannan ba daidai ba ne, domin mutane da suka yi aure ne kawai ya kamata su kwana da juna. Wannan mugun abin da Shechem ya yi wa Dinah ya jawo ƙarin masifu.

Da yayyen Dinah suka ji abin da ya faru, suka yi fushi ƙwarai. Biyu cikinsu, Simeon da Lawi, sun fusata ƙwarai har suka ɗauki takobi suka tafi birnin suka kai wa mutanen harin ba zata. Su da ’yan’uwansu suka kashe Shechem da dukan sauran mutanen. Yakubu ya yi fushi ƙwarai domin ’ya’yansa sun yi wannan mugun abin.

Ta yaya wannan masifar ta fara? Domin Dinah ta yi abota da mutanen da ba sa bin dokar Allah. Ba za mu so mu yi irin waɗannan abokanan ba, ko ba haka ba?

Farawa 34:1-31.