Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 21

’Yan’uwan Yusufu Ba Sa Son Shi

’Yan’uwan Yusufu Ba Sa Son Shi

DUBI baƙin ciki na wannan yaro kuma babu abin da zai iya yi. Yusufu ke nan. Yayyensa sun sayar da shi ga waɗannan mutane da suke kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Masar. A can Yusufu zai zama bawa. Me ya sa waɗannan ’yan ubansa suka yi wannan mummunar abu? Domin suna kishin Yusufu ne.

Babansu Yakubu yana son Yusufu sosai, sosai. Ya nuna masa ƙauna da ya sa ya yi masa doguwar riga kyakkyawa. Sa’ad da yayyensa 10 suka ga yadda Yakubu yake son Yusufu, suka fara kishinsa kuma suka ƙi shi. Da wani dalili kuma da ya sa ba sa son shi.

Yusufu ya yi mafarki sau biyu. A dukan mafarkai biyu da ya yi ’yan’uwan nasa suna rusuna masa. Da Yusufu ya gaya wa ’yan’uwan nasa waɗannan mafarkai, ƙiyayyar ta su ta yi tsanani.

Wata rana da yayyen nasa suna kula da tumakin babansu, Yakubu ya tura Yusufu ya je ya duba lafiyarsu. Sa’ad da ’yan’uwan nasa suka hango sa yana zuwa, wasu cikinsu suka ce: ‘Mu kashe shi!’ Amma sai Reuben ɗan farin, ya ce: ‘A’a, kada ku yi haka!’ Maimakon haka, suka jefa Yusufu cikin busashiyar rijiya. Sai suka zauna suna shawarar abin da za su yi da shi.

A wannan lokacin kuma sai ga wasu Isma’ilawa suna wucewa. Yahuda ya ce wa sauran: ‘Mu sayar da shi ga Isma’ilawa.’ Abin da suka yi ke nan. Suka sayar da shi a kan azurfa 20. Wannan ƙeta ce ƙwarai!

To menene ’yan’uwan nasa za su gaya wa babansu? Sai suka yanka akuya suka tsoma kyakkyawar rigar Yusufu cikin jinin akuyar. Sai suka ɗauki rigar suka kai wa babansu Yakubu suka ce: ‘Mun sami wannan. Ka dubu ka gani ko rigar Yusufu ce.’

Yakubu ya ga ita ce. Yana kuka yana cewa: ‘Wata dabbar daji ta kashe Yusufu.’ Abin da ’yan’uwan Yusufu suke so babansu ya yi tsammani ke nan. Yakubu ya yi baƙin ciki ƙwarai. Ya yi kuka na kwana da kwanaki. Amma Yusufu bai mutu ba. Bari mu ga abin da ya faru da shi a inda aka kai shi.

Farawa 37:1-35.