Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 22

An Jefa Yusufu A Kurkuku

An Jefa Yusufu A Kurkuku

YUSUFU yana da shekara 17 sa’ad da aka kai shi ƙasar Masar. A nan ne aka sayar da shi ga wani mutumi mai suna Fotifa. Fotifa ma’aikaci ne na sarkin Masar, wanda ake kira Fir’auna.

Yusufu ya yi aiki da zuciya ɗaya ga maigidansa, Fotifa. Saboda haka sa’ad da Yusufu ya girma, Fotifa ya sa shi iko bisa dukan gidansa. To, me ya sa kuma Yusufu yake cikin fursuna? Domin matar Fotifa ce.

Yusufu ya girma ya zama kyakkyawan mutum, sai matar Fotifa ta so ya kwana da ita. Amma Yusufu ya sani cewa wannan ba daidai ba ne, sai ya ƙi. Matar Fotifa ta yi fushi sosai. Sa’ad da mijinta ya dawo gida, sai ta yi masa ƙarya tana cewa: ‘Munafukin nan Yusufu ya yi ƙoƙarin ya kwana da ni!’ Fotifa ya yarda da abin da matarsa ta ce, ya yi fushi ƙwarai da Yusufu. Saboda haka aka jefa shi kurkuku.

Nan da nan mai kula da kurkukun ya ga cewa Yusufu mutumin kirki ne. Saboda haka ya ba shi ikon kula da dukan sauran fursunonin. Ba da daɗewa ba Fir’auna ya yi fushi da mai shayarwa da kuma mai yi masa tuya, sai ya jefa su cikin kurkuku. A cikin dare ɗaya sai dukansu biyu suka yi mafarki na musamman, amma ba su san abin da mafarkin yake nufi ba. Da gari ya waye sai Yesu ya ce musu: ‘Ku gaya mini mafarkinku.’ Da suka gaya masa, tare da taimakon Allah Yusufu ya gaya musu ma’anar mafarkinsu.

Ga mai shayarwa, Yusufu ya ce: ‘A cikin kwana uku za a fitar da kai daga kurkuku, kuma za ka koma bakin aikinka na shayarwa.’ Sai kuma Yusufu ya gaya masa: ‘Ka gaya wa Fir’auna game da ni, ka taimake ni in fita daga wannan wuri.’ Amma ga mai tuya, Yusufu ya ce: ‘A cikin kwana uku, Fir’auna zai sa a sare kanka.’

A cikin kwanaki uku abin ya faru kamar yadda Yusufu ya faɗa. Fir’auna ya sa aka sare kan mai tuya. Amma mai shayarwa aka salame shi daga kurkuku ya koma yana yi wa sarki aiki. Amma sai mai shayarwa ya mance da Yusufu! Bai gaya wa Fir’auna game da Yusufu ba, Yusufu ya ci gaba da zama a fursuna.

Farawa 39:1-23; 40:1-23.