Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 23

Mafarkan Fir’auna

Mafarkan Fir’auna

SHEKARU biyu sun riga sun shige, kuma Yusufu yana nan cikin kurkuku. Mai shayarwa bai tuna da shi ba. Sai Fir’auna ya yi mafarkai biyu masu muhimmanci cikin wani dare, ya yi mamaki ko menene waɗannan suke nufi. Ka gan sa a nan yana barci? Da safiya ta yi Fir’auna ya tattara dukan mutanensa masu hikima ya gaya musu mafarkan da ya yi. Amma babu wanda ya iya gaya masa ma’anar mafarkinsa.

Sai mai shayarwa ya tuna da Yusufu. Ya gaya wa Fir’auna: ‘Sa’ad da nake kurkuku da akwai wani mutum da zai iya faɗin ma’anar mafarkai.’ Fir’auna ya sa aka fito da Yusufu babu ɓata lokaci.

Fir’auna ya gaya wa Yusufu game da mafarkansa: ‘Na ga shanu bakwai kyawawa masu ƙiba. Sai kuma na ga wasu bakwai ramammu. Sai kuma ramammun suka cinye masu ƙiban.

‘A mafarkina na biyu na ga zangarnu bakwai cikakku da suka ƙosa sun fito daga kara ɗaya. Sai kuma na ga wasu bakwai sirara. Sai kuma busassun suka fara haɗiye bakwai kyawawan.’

Yusufu ya gaya wa Fir’auna: ‘Mafarkai biyun suna nufin abu ɗaya ne. Shanu bakwai masu ƙiba da kuma zangarnu bakwai cikakku suna nufin shekaru bakwai, kuma shanu bakwai ƙanjamammu da zangarnu bakwai busassu su ma na nufin wasu shekarun bakwai. Za a yi shekara bakwai da za a sami abinci ƙwarai a ƙasar Masar. Sai kuma a yi shekaru bakwai na ƙarancin abinci.’

Sai Yusufu ya gaya wa Fir’auna: ‘Ka zaɓi mutum mai hikima ka sanya shi bisa sha’anin tara abinci a cikin shekarun nan bakwai na yalwa. Saboda kada mutane su mutu don yunwa a shekaru bakwai na yunwa.’

Fir’auna ya ji daɗin shawarar. Sai ya zaɓi Yusufu ya tara abinci, kuma ya yi ajiyarsu. Yusufu ya zama shi ne na biye da Fir’auna wajen martaba a ƙasar Masar.

Bayan shekara takwas, a lokacin yunwa, Yusufu ya ga wasu mutane suna zuwa. Ka san ko su wanene ne? ’Yan’uwansa ne su 10! Babansu Yakubu ya aiko su ƙasar Masar domin abincinsu ya kusa ƙarewa a ƙasarsu Kan’ana. Yusufu ya gane ’yan’uwansa, amma su ba su gane shi ba. Ka san abin da ya sa? Domin Yusufu ya girma kuma yana sanye da wasu irin tufafi.

Yusufu ya tuna cewa sa’ad da yake yaro ya yi mafarki cewa ’yan’uwansa sun zo suna durƙusa masa. Ka tuna cewa ka karanta wannan kuwa? Da haka Yusufu ya fahimci cewa Allah ne ya aiko shi ƙasar Masar domin kyakkyawan dalili. Me kake tsammani Yusufu ya yi? Bari mu gani.

Farawa 41:1-57; 42:1-8; 50:20.