Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 24

Yusufu Ya Gwada ’Yan’uwansa

Yusufu Ya Gwada ’Yan’uwansa

YUSUFU yana so ya sani ko har yanzu ’yan’uwansa goma azzalumai ne masu ƙeta. Sai ya ce: ‘Ku ’yan leƙen asiri ne. Kun zo ne ku leƙi asirin ƙasarmu.’

Suka ce: ‘A’a mu ba ’yan leƙen asiri ba ne. Mu mutanen kirki ne. Mu duka ’yan’uwa ne. Mu 12 ne, amma ɗayanmu ya mutu, kuma autanmu yana tare da babanmu a gida.’

Yusufu ya yi kamar bai yarda da abin da suka ce ba. Ya saka Saminu a cikin kurkuku, ya ƙyale sauran suka koma gida da abinci. Amma ya gaya musu: Sa’ad da za ku sake zuwa, ku zo da autanku.’

Sa’ad da suka koma ƙasarsu Kan’ana, ’yan’uwansa suka gaya wa babansu Yakubu dukan abin da ya faru. Yakubu ya yi baƙin ciki. Ya yi kuka yana cewa: ‘Babu Yusufu kuma ga shi yanzu babu Saminu. Ba zan ƙyale ku ku ɗauki autanku Biliyaminu ba.’ Amma sa’ad da abincinsu ya fara ƙarewa, Yakubu ya ƙyale su su tafi da Biliyaminu ƙasar Masar saboda su ƙaro abinci.

Sai Yusufu ya ga ƙaninsa yana zuwa. Ya yi farin cikin ganin ƙaninsa Biliyaminu. Hakika, dukansu ba su san cewa wannan babban mutumin Yusufu ne ba. Sai Yusufu ya yi wani abu ya gwada ’yan’uwansa goma.

Ya sa bayinsa suka cika dukan buhunansu da abinci. Amma ba tare da ya gaya musu ba, ya sa aka saka ƙoƙonsa na azurfa a cikin buhun Biliyaminu. Bayan sun yi ɗan nisa, Yusufu ya sa bayinsa suka bi su. Da suka tarar da su, sai bayin suka ce: ‘Me ya sa kuka saci ƙoƙon azurfa na ubangijinmu?’

‘Ba mu saci ƙoƙo ba,’ in ji su. ‘Idan kuka sami ƙoƙon a wurin ɗaya daga cikinmu ku kashe shi.’

Saboda haka bayin suka bincika dukan buhunansu, sai suka sami ƙoƙon a cikin buhun Biliyaminu, kamar yadda ka gani a nan. Bayin suka ce: ‘Ku sauran ku yi tafiyarku, amma Biliyaminu dole ya bi mu.’ Menene ’yan’uwansa 10 za su yi yanzu?

Suka koma tare da Biliyaminu zuwa gidan Yusufu. Yusufu ya gaya wa ’yan’uwansa: ‘Dukanku ku koma ƙasarku, amma Biliyaminu zai zama bawana.’

Sai Yahuda ya yi magana, ya ce: ‘Idan na koma gida ba tare da yaron ba, babana zai mutu domin yana ƙaunar yaron sosai. Saboda haka, don Allah bari ni in zama bawanka, ka ƙyale yaron ya koma gida.’

Yusufu ya ga cewa ’ya’uwansa sun sake halinsu. Ba azzalumai ba ne masu ƙeta kamar dā. Bari mu ga abin da Yusufu ya yi.

Farawa 42:9-38; 43:1-34; 44:1-34.