Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 28

Yadda Aka Ceci Musa Yana Jariri

Yadda Aka Ceci Musa Yana Jariri

DUBI jaririn nan yana kuka, ya riƙe yatsar wannan matar. Musa ne. Ka san ko wacece wannan kyakkyawar matar? ’Yar Fir’auna ce gimbiyar ƙasar Masar.

Mamar Musa ta ɓoye jaririnta har sai da ya kai wata uku, domin ba ta son Masarawa su kashe shi. Amma ta sani cewa za su iya samun Musa, saboda haka ta yi wani abu domin ta cece shi.

Ta ɗauki kwando ta gyara domin kada ruwa ya shiga ciki. Sai ta saka Musa a ciki, ta ajiye shi a cikin dogayen ciyayi na bakin Kogin Nilu. Aka gaya wa yayar Musa, Maryamu ta tsaya a kusa ta ga abin da zai faru.

Jim kaɗan sai ga yar Fir’auna ta zo wanka a Kogin Nilu. Kwaram sai ta ga kwandon a cikin ciyayin. Ta gaya wa ɗaya daga cikin bayinta mata: ‘Ki je ki ɗauko mini wancan kwandon.’ Sa’ad da gimbiyar ta buɗe kwandon, sai ta ga kyakkyawan jariri! Jariri Musa yana kuka, sai gimbiyar ta ji tausayinsa. Ba ta so a kashe shi.

Sai Maryamu ta matso kusa. Ka ganta a cikin hoton. Maryamu ta tambayi ’yar Fir’auna: ‘In je in kirawo miki Ba’isra’iliya ta kula miki da jaririn?’

‘Maza ki tafi’ in ji gimbiyar.

Sai Maryamu ta yi sauri ta je ta gaya wa mamarta. Sa’ad da mamar Musa ta zo wurin gimbiyar, gimbiyar ta ce mata: ‘Ga wannan yaron ki yi renonsa, zan biya ki.’

Saboda haka, mamar Musa ta kula da ɗanta. Daga baya sa’ad da Musa ya ɗan girma, ta kai shi wurin ’yar Fir’auna, ita kuwa ta ɗauke shi kamar ɗanta. Haka ne ya kasance Musa ya girma a gidan Fir’auna.

Fitowa 2:1-10.