Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 29

Dalilin Da Ya Sa Musa Ya Gudu

Dalilin Da Ya Sa Musa Ya Gudu

DUBI Musa yana gudu daga ƙasar Masar. Ka ga waɗannan mutanen da suke binsa? Ka san abin da ya sa suke so su kashe Musa? Bari mu ga ko za mu iya binciko dalilin.

Musa ya girma a gidan Fir’auna sarkin Masar. Ya zama mutum mai hikima ƙwarai mai martaba. Musa ya sani cewa shi ba Bamasare ba ne, amma iyayensa na ainihi bayi ne Isra’ilawa.

Wata rana sa’ad da yake ɗan shekara 40, Musa ya je ya ga yadda mutanensa suke ji da aiki. Yadda ake gana musu azaba abin tausayi ne. Ya ga wani Bamasare yana dukan wani bawa Ba’isra’ile. Musa ya waiwaya, da ya ga babu kowa, sai ya bugi Bamasaran, sai Bamasaren ya mutu. Sai Musa ya ɓoye gawarsa cikin yashi.

Washegari Musa ya je ya sake ganin mutanensa. Yana tunanin zai iya taimakonsu domin kada su ci gaba da zama bayi. Amma sai ya ga Isra’ilawa biyu suna faɗa, saboda haka Musa ya gaya wa mai laifin: ‘Me ya sa kake dukan ɗan’uwanka?’

Sai mutumin ya ce: ‘Wa ya naɗa ka sarki da alƙali bisanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe wancan Bamasaren.’

Sai Musa ya ji tsoro. Ya sani cewa mutane sun san abin da ya yi wa Bamasaren. Har Fir’auna ya ji abin da ya faru, sai ya aiki mutane su kashe Musa. Abin da ya sa ke nan Musa ya gudu daga ƙasar Masar.

Sa’ad da Musa ya bar ƙasar Masar, ya yi nesa har ƙasar Midiyan. A nan ya sadu da iyalin Jethro, ya auri ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata mai suna Zipporah. Musa ya zama mai kiwo yana kiwon tumakin Jethro. Ya zauna a ƙasar Midiyan na shekara arba’in. Shekarunsa suka cika 80 da haihuwa. Sai wata rana, sa’ad da Musa yake kula da tumakin Jethro, wani abin mamaki ya faru da ya canja rayuwar Musa. Ka juya zuwa shafi na gaba, bari mu ga wannan abin mamakin.

Fitowa 2:11-25; Ayukan Manzanni 7:22-29.