Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 31

Musa Da Haruna Sun Je Wurin Fir’auna

Musa Da Haruna Sun Je Wurin Fir’auna

SA’AD da Musa ya koma ƙasar Masar, ya gaya wa wansa Haruna game da mu’ujizar. Sa’ad da Musa da Haruna suka nuna wa Isra’ilawa dukan waɗannan mu’ujizar, mutanen suka yarda cewa Jehobah yana tare da su.

Sai Musa da Haruna suka je wurin Fir’auna. Suka gaya masa: ‘Jehobah Allah na Isra’ila ya ce, “Ka ƙyale mutane na na kwana uku, saboda su bauta mini a cikin daji.”’ Amma Fir’auna ya amsa: ‘Ni ban yarda da Jehobah ba. Kuma ba zan ƙyale Isra’ilawa su tafi ba.’

Fir’auna ya fusata, domin mutanen suna neman hutu daga aiki domin su bauta wa Jehobah. Saboda haka ya tilasta musu su yi aiki ma fiye da dā. Isra’ilawa suka ga laifin Musa domin yadda ake gana musu azaba, kuma Musa bai yi farin ciki ba. Amma Jehobah ya gaya masa cewa kada ya damu. ‘Zan sa Fir’auna ya ƙyale mutane na,’ in ji Jehobah.

Musa da Haruna suka sake komawa wurin Fir’auna. A wannan lokacin suka yi mu’ujiza. Haruna ya jefar da sandansa sai ya zama babban maciji. Amma masu hikimar Fir’auna ma suka jefar da sandunan su suka zama macizai. Amma ka gani! Macijin Haruna yana cinye na masu hikiman. Duk da haka Fir’auna ya ƙi ƙyale Isra’ilawa su tafi.

Sai lokaci ya yi da Jehobah zai koya wa Fir’auna hankali. Ka san yadda ya yi haka? Ta wurin kawo annoba 10, ko kuma manyan masifu bisa ƙasar Masar.

Bayan kowane annoba, sai Fir’auna ya sa a kira Musa, ya ce: ‘Ka dakatar da annobar, zan ƙyale Isra’ilawa su tafi.’ Amma bayan annobar ta ƙare, sai Fir’auna ya ƙi. Ya ƙi ƙyale Isra’ilawa su tafi. Amma a ƙarshe, bayan annoba ta 10, Fir’auna ya ƙyale Isra’ilawa suka tafi.

Ka san dukan annoba 10? Ka juya zuwa shafi na gaba bari mu koya game da su.

Fitowa 4:27-31; 5:1-23; 6:1-13, 26-30; 7:1-13.