Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 32

Annoba Guda Goma

Annoba Guda Goma

DUBI waɗannan hotunan. Kowane ya nuna irin annoba da Jehobah ya kawo bisa ƙasar Masar. A hoto na farko za ka ga Haruna yana buga Kogin Nilu da sandansa. Bayan da ya yi haka, ruwan da yake kogin ya zama jini. Kifaye suka mutu, kogin ya fara wari.

Na gaba, Jehobah ya sa kwaɗi suka fito daga Kogin Nilu. Suka shiga ko’ina, wurin dafuwa, a kan gadajen mutane, kwanonin dafuwa, ko’ina. Da kwaɗin suka mutu Masarawa suka tara su tari mai yawa, ƙasar ta cika da ɗoyi dominsu.

Sai Haruna ya buga ƙasa da sandarsa, sai kura ta zama ƙananan ƙwari masu kama da kwarkwata. Waɗannan ƙananan ƙwari ne masu tashi masu cizo. Ƙwarin sune annoba ta uku bisa ƙasar Masar.

Annoba na gaba Masarawa kawai ya shafa bai shafi Isra’ilawa ba. Na huɗu annobar manyan ƙudaje ne da suka yi ta shiga gidajen Masarawa. Annoba ta biyar bisa dabbobi ne. Shanu da tumaki da awakin Masarawa suka mutu.

Sai Musa da Haruna suka ɗebi toka suka watsa a sama. Suka sa mugayen marurai suka riƙa fitowa a jikin mutane da dabbobi. Wannan shi ne annoba ta shida.

Bayan wannan Musa ya ɗaga hannunsa sama, sai Jehobah ya aiko da aradu da ƙanƙara. Wannan shi ne ruwa da ƙanƙara mai muni da Masarawa suka taɓa gani.

Annoba ta takwas na fari ne masu yawa. Ba a ta taɓa ganin fari masu yawa haka ba. Farin suka cinye dukan wani abin da ƙanƙarar ta bari.

Annoba na tara duhu ne. Kwana uku duhu ya rufe ƙasar, amma da haske wurin da Isra’ilawa suke.

A ƙarshe, Allah ya gaya wa mutanensa su yafa jini ɗan akuya ko na ɗan rago a ƙofarsu. Sai mala’ikan Allah ya ƙetare. Sa’ad da mala’ikan ya ga jinin, ba zai kashe kowa ba a gidan. Amma a dukan gidajen da babu jini a ƙofar, mala’ikan Allah ya kashe ɗan farin mutum da dabba. Wannan shi ne annoba ta 10.

Bayan wannan annoba ta goma, Fir’auna ya gaya wa Isra’ilawa su tafi. Mutanen Allah duka suna shirye su tafi, kuma a cikin wannan daren suka fita daga Masar.

Fitowa surori 7 zuwa 12.