Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 34

Sabon Abinci

Sabon Abinci

KA SAN abin da waɗannan mutanen suke tsinta daga ƙasa? Ya yi kama da ƙanƙara. Fari ne, ba shi da kauri kuma ƙwayoyi ne. Amma ba ƙanƙara ba ce, abinci ne.

Bai wuce wata ɗaya ba da Isra’ilawa suka bar ƙasar Masar. Suna cikin daji. Kuma babu abinci sosai a nan, saboda haka mutanen suka fara mita, suna cewa: ‘Da ma Jehobah ya kashe mu a ƙasar Masar. Aƙalla, a can muna samun dukan irin abincin da muke so.’

Saboda haka, Jehobah ya ce: ‘Zan zuɓo da abinci daga sama.’ Haka kuwa Jehobah ya yi. Washegari da Isra’ilawan suka ga wannan farin abin da suka zubo, suka fara tambayar junansu: ‘Menene wannan?’

Musa ya ce: ‘Wannan shi ne abincin da Jehobah ya ba ku ku ci.’ Mutanen suka kira shi MANNA. Ɗanɗanonsa kamar na waina ne da aka yi da zuma.

‘Ku ɗebi iyakar abin da kowa zai iya ci,’ Musa ya gaya wa mutanen. A kowace safiya sai su je su ɗiba. Amma, idan rana ta fito ta yi zafi, manna da suka ƙyale a ƙasa sai ya narke.

Musa kuma ya ce musu: ‘Kada kowa ya ɗiba domin gobe.’ Amma wasu mutane ba su saurara ba. Ka san abin da ya faru? Washegari manna da suka ajiye sai ya cika da tsutsa, ya fara wari!

Amma da rana ɗaya a mako, da Jehobah ya gaya wa mutane su ɗebi manna domin abincinsu na kwana biyu. Wannan ita ce rana ta shida. Kuma Jehobah ya ce su ci su rage domin gobe, domin ba zai zuɓo da manna ba a rana ta bakwai. Sa’ad da suka ajiye manna domin rana ta bakwai, bai cika da tsutsa ba kuma ba ya wari! Wannan wani abin al’ajabi ne!

A dukan shekaru da Isra’ilawa suka yi a cikin daji Jehobah ya ciyar da su da manna.

Fitowa 16:1-36; Litafin Lissafi 11:7-9; Joshua 5:10-12.