Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 36

Ɗan Maraƙin Zinariya

Ɗan Maraƙin Zinariya

KAIYA, kaiya! Menene mutanen nan suke yi a nan? Suna bauta wa ɗan maraƙi! Me ya sa suke haka?

Da yake Musa ya daɗe a kan dutse, sai mutanen suka ce: ‘Ba mu san abin da ya sami Musa ba. Saboda haka, bari mu ƙera wa kanmu allah da zai fitar da mu daga wannan ƙasar.’

‘To shi ke nan,’ in ji Haruna yayan Musa. ‘Ku cicciro ’yan kunnen zinariyar da ke kunnuwanku ku kawo mini.’ Sa’ad da mutanen suka yi haka, Haruna ya narkar da su, ya yi ɗan maraƙin zinariya da su. Sai mutanen suka ce: ‘Wannan Allahnmu ne, shi ya fito da mu daga ƙasar Masar!’ Sai Isra’ilawan suka yi babban biki, suka kuma bauta wa ɗan maraƙi na zinariya.

Sa’ad da Jehobah ya ga haka, sai ya yi fushi ƙwarai. Saboda haka ya ce wa Musa: ‘Ka yi sauri ka sauka. Jama’arka suna mummunan aiki. Sun manta da dokokina kuma suna yi wa ɗan maraƙi sujada.

Musa ya yi sauri ya sauko daga kan dutsen. Sa’ad da ya yi kusa, wannan shi ne abin da ya gani. Mutanen suna rawa suna waƙa a gaban ɗan maraƙin na zinariya! Musa ya yi fushi sosai da ya jefar da allunan na dutse da suke ɗauke da dokokin, suka faɗi suka farfashe. Sai ya ɗauki ɗan maraƙin ya narke shi. Sai ya niƙa shi ya zama gari.

Mutanen sun yi mugun abu. Saboda haka Musa ya gaya wa wasu mutanen su zaro takubbansu. ‘Miyagun mutane da suka bauta wa ɗan maraƙin dole ne a kashe su,’ in ji Musa. Sai mutanen suka kashe wajen mutane 3,000! Wannan bai nuna ba ne cewa ya kamata mu mai da hankali mu bauta wa Jehobah shi kaɗai?

Fitowa 32:1-35.