Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 37

Tanti Domin Bauta

Tanti Domin Bauta

KA SAN ko menene wannan ginin? Tanti ne na musamman domin bautar Jehobah. Ana kuma kiransa mazauni. Mutanen sun kammala gina shi shekara ɗaya bayan sun fita daga ƙasar Masar. Ka san ko ra’ayin wanene ne su gina shi?

Ra’ayin Jehobah ne. Sa’ad da Musa yake kan Dutsen Sinai, Jehobah ya gaya masa yadda zai gina shi. Ya gaya masa ya gina shi domin ya kasance da sauƙin warwarewa. A haka za a iya ɗaukansa zuwa wani wuri dabam, a sake harhaɗawa. Saboda haka duk inda Isra’ilawa suka yi zango a cikin daji, za su tafi da shi.

Idan ga dubi cikin ɗan ɗaki da ke ƙarshen tantin za ka ga akwati. Ana kiran wannan akwatin alkawari. Yana da mala’iku biyu da aka yi da zinariya, a kowane ɓangare. Allah ya sake rubuta Dokokin Goma a kan wasu alluna biyu domin Musa ya fasa na farkon. Kuma waɗannan duwatsun suna cikin sunduƙin alkawarin. Da kuma tukunya da manna a cikinta. Ka tuna ko menene manna?

Haruna yayan Musa ne Jehobah ya zaɓa ya zama babban firist. Ya shugabanci mutanen wajen bauta wa Jehobah. Kuma ’ya’yansa ma suka zama firistoci.

Yanzu dubi babban ɗakin tantin. Ya yi biyun ƙaramin ɗakin. Ka ga akwati da hayaki yake tashi daga cikinsa? Wannan bagadi ne inda firist yake ƙona abubuwa masu ƙamshi da ake kira turaren hayaƙi. Akwai kuma fitila mai rassa bakwai. Abu na uku kuma da ke cikin ɗakin teburi ne. Ana ajiye burodi 12 a kai.

A cikin filin mazaunin kuma da akwai babbar tasa da take cike da ruwa. Firistoci suna amfani da shi domin wanki. Da akwai kuma babban bagadi. A nan ake ƙona dabbobin da aka yanka domin hadaya ga Jehobah. Tantin yana tsakiyar inda Isra’ilawa suka yi zango.

Fitowa 25:8-40; 26:1-37; 27:1-8; 28:1; 30:1-10, 17-21; 34:1, 2; Ibraniyawa 9:1-5.