Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 39

Sandan Haruna Ya Yi Fure

Sandan Haruna Ya Yi Fure

KA DUBI furanni da kuma ’ya’yan almon da suka fito a kan wannan sanda. Wannan sandan Haruna ne. Waɗannan furanni da kuma ’ya’yan almon da ke kan sandan Haruna sun fito ne cikin dare ɗaya! Bari mu ga abin da ya sa.

Isra’ilawa sun daɗe suna yawo a yanzu cikin daji. Wasu cikin mutane suna gani bai kamata Musa ya ci gaba da zama shugaba ba, ko kuma Haruna ya zama babban firist. Kora yana cikin waɗanda suke wannan tunani, shi da Dathan, Abiram da kuma wasu shugabanni 250. Dukan waɗannan suka zo suka gaya wa Musa: ‘Me ya sa ka ɗaukaka kanka fiye da dukanmu?’

Musa ya gaya wa Kora da mabiyansa: ‘Gobe da safe, kowane mutum ya ɗauki kaskon wutarsa da turare a ciki. Sa’annan ku zo mazaunin Jehobah. Za mu ga wanda Jehobah ya zaɓa.’

Washegari Kora da mabiyansa 250 suka hallara a mazauni. Wasu mutane da yawa suka zo su goyi bayan waɗannan mutane. Jehobah ya yi fushi sosai. ‘Ku ƙaurace wa tantin waɗannan miyagun mutane,’ in ji Musa. ‘Kada ku taɓa kome nasu.’ Mutanen suka saurara, suka ƙaurace wa tantin Kora, Dathan da Abiram.

Sai Musa ya ce: ‘Ta haka za ku san wanda Jehobah ya zaɓa. Ƙasa za ta tsage ta haɗiye wannan miyagun mutane.’

Musa yana rufe baƙinsa, sai ƙasa ta tsage. Tantin Kora da dukan abin da ke na shi da kuma Dathan da Abiram da dukan waɗanda suke tare da su ƙasa ta haɗiye su, ta rufe bakinta. Sa’ad da mutanen suka ji kukan waɗanda suke faɗawa rami, suka fara ihu: ‘Mu gudu, ƙasa za ta haɗiye mu muma!’

Kora da mabiyansa 250 suna tsaye kusa da mazauni. Sai Jehobah ya aiko da wuta ta ƙona su. Sai Jehobah ya gaya wa ɗan Haruna Eleazar ya kwashi kaskon wuta na mutanen ya yi marufi fale-fale ga bagadi. Wannan marufi zai riƙa tuna wa Isra’ilawa cewa Haruna ne kawai da ’ya’yansa za su zama firistoci na Jehobah.

Amma Jehobah yana so ya kawar da dukan wata shakka cewa Haruna ne da ’ya’yansa ya zaɓa su zama firistoci. Saboda haka ya gaya wa Musa: ‘Bari kowane shugaban ƙabila na Isra’ilawa su kawo sanduna. Kuma ga ƙabilar Lawiyawa, Haruna ya kawo sandarsa. Sai ka saka dukan sandunan cikin mazauni a gaban sunduƙin alkawari. Sandan mutumin da na zaɓa ya zama firist zai yi furanni.’

Da Musa ya duba da safe, sandan Haruna ne da furanni da kuma ’ya’yan almon a kai! Ka ga abin da ya sa Jehobah ya sa sandan Haruna ta yi furanni?

Litafin Lissafi 16:1-49; 17:1-11; 26:10.