Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 41

Macijin Tagulla

Macijin Tagulla

WANNAN ya yi kama ne da macijin gaskiya da ke naɗe a jikin wannan gungume? A’a. An yi macijin ne da tagulla. Jehobah ya gaya wa Musa ya ɗaura shi a sama domin mutane su gani su rayu. Amma sauran macizan da suke ƙasa na gaskiya ne. Suna cizon mutane suna sa su rashin lafiya. Ka san abin da ya sa?

Domin Isra’ilawa sun yi wa Allah da kuma Musa gunaguni. Suna gunaguni suna cewa: ‘Me ya sa ka fito da mu daga ƙasar Masar domin mu mutu a wannan dajin? Babu abinci ko ruwan sha a nan. Kuma ba za mu iya ci gaba da cin wannan manna ba kuma.’

Amma manna abinci ne mai kyau. Jehobah ya yi musu tanadinsa ta wajen mu’ujiza. Ta wajen mu’ujiza kuma ya ba su ruwan sha. Duk da haka mutanen ba su yi godiya ga Allah ba domin yadda yake kula da su. Saboda haka Jehobah ya aika da waɗannan macizai masu dafi su yi musu horo. Macizan suka ciccije su, kuma da yawa cikinsu suka mutu.

A ƙarshe mutanen suka je wurin Musa suka ce: ‘Mun yi zunubi, domin mun yi gunaguni game da Jehobah da kuma kai. Ka yi wa Jehobah addu’a ya ɗauke mana waɗannan macizai.’

Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutanen. Sai Jehobah ya gaya wa Musa ya yi wannan maciji na tagulla. Ya gaya masa ya ɗaura a kan gungume, kuma dukan wanda maciji ya cije shi ya kalli wannan na tagulla. Musa ya yi daidai abin da Allah ya gaya masa. Kuma mutanen da maciji ya cije su suka kalli macijin tagulla kuma suka sami lafiya.

Da darasi da za mu koya daga nan. Dukanmu muna kama ne da waɗannan Isra’ilawa waɗanda maciji ya cije su. Dukanmu muna kan hanyar mutuwa. Idan ka duba, za ka ga cewa mutane suna tsufa, suna ciwo, kuma suna mutuwa. Hakan ya kasance ne domin mata da miji na farko, Adamu da Hauwa’u, sun juya wa Jehobah baya, kuma dukanmu ’ya’yansu ne. Amma kuma Jehobah ya yi mana tanadin hanyar da za mu rayu har abada.

Jehobah ya aiko da Ɗansa, Yesu Kristi, zuwa duniya. Aka rataye Yesu a kan gungume, domin mutane da yawa suna tsammanin shi mugun mutum ne. Amma Jehobah ya ba da Yesu ne domin ya cece mu. Idan muka bi shi, za mu sami rai na har abada. Za mu koyi game da wannan a gaba.

Litafin Lissafi 21:4-9; Yohanna 3:14, 15.