Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 48

Gibeyonawa Masu Hikima

Gibeyonawa Masu Hikima

YAWANCIN biranen da suke Kan’ana yanzu suna da shirin yaƙan Isra’ila. Suna tsammanin za su yi nasara. Amma mutanen da suke birnin Gibeyon na kusa ba su yi tunanin haka ba. Sun yarda cewa Allah yana taimakon Isra’ilawa, kuma ba sa son su yaƙi Allah. Saboda haka, ka san abin da Gibeyonawan suka yi?

Suka shawarta su bayyana kamar daga wuri mai nisa suka zo. Wasu mutane suka sa tsofaffin tufafi da takalma da suka mutu. Suka ɗora wa jakunansu tsofaffin buhuna, suka ɗauki burodi da suka bushe. Sai suka je wajen Joshua suka ce: ‘Mun zo ne daga ƙasa mai nisa, domin mu ji game da Allahnku mai girma, Jehobah. Mun ji dukan abubuwa da ya yi a ƙasar Masar. Saboda haka dattawanmu suka ce mana mu ɗauki guzuri mu zo mu gaya muku: “Mu bayinku ne. Ku yi mana alkawari cewa ba za ku yaƙe mu ba.” Kun ga cewa tufafinmu sun tsufa domin doguwar tafiya kuma burodinmu duka sun bushe.’

Joshua da kuma sauran dattawa suka yarda da abin da Gibeyonawan suka ce. Saboda haka suka yi musu alkawari cewa ba za su yaƙe su ba. Amma bayan kwana uku suka fahimci cewa Gibeyon ba shi da nisa.

‘Me ya sa kuka ce mana kun fito daga ƙasa mai nisa?’ Joshua ya tambaye su.

Gibeyonawan suka amsa: ‘Mun yi haka ne domin an gaya mana cewa Allahnku Jehobah ya yi alkawari zai ba ku dukan ƙasar Kan’ana. Soboda haka muna tsoron za ku kashe mu.’ Amma Isra’ilawa suka kiyaye alkawarinsu, ba su kashe Gibeyonawan ba. Maimakon haka suka mai da su bayinsu.

Sarkin Urushalima ya yi fushi ƙwarai da Gibeyonawa domin sun sulhunta da Isra’ila. Saboda haka ya gaya wa wasu sarakuna huɗu: ‘Ku zo ku taimake ni mu yaƙi Gibeyon.’ Abin da waɗannan sarakuna biyar suka yi ke nan. Gibeyonawan sun yi hikima ne da suka yi sulhu da Isra’ila, da ya sa waɗannan sarakuna za su yaƙe su? Bari mu gani.

Joshua 9:1-27; 10:1-5.