Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 49

Rana Ta Tsaya Wuri Ɗaya

Rana Ta Tsaya Wuri Ɗaya

DUBI Joshua. Yana cewa: ‘Rana, tsaya wuri ɗaya!’ Kuma rana ta tsaya wuri ɗaya. Ta tsaya daidai tsakar rana har yini guda. Jehobah ya sa ya faru! Amma bari mu ga abin da ya sa Joshua yake so rana ta ci gaba da haskakawa.

Sa’ad da miyagun sarakuna biyar na ƙasar Kan’ana suka fara yaƙi da Gibeyonawa, Gibeyonawan suka aiki wani mutum ya nemi taimako wajen Joshua. ‘Ku zo wurinmu da sauri!’ in ji shi. ‘Ku cece mu! Dukan sarakuna da suke kan tuddai sun zo su yaƙi bayinku.’

Nan da nan Joshua da mayaƙansa suka tafi. Sun yi tafiya dukan dare. Da suka isa Gibeyon sojojin dukan sarakuna biyar suka tsorata suka fara gudu. Sai Jehobah ya zubo da manyan ƙanƙara daga sama, ƙanƙarar ta kashe sojoji fiye da waɗanda mayaƙan Joshua suka kashe.

Joshua ya lura cewa ba da daɗewa ba rana za ta faɗi. Dare zai yi, kuma sojojin miyagun sarakuna biyar ɗin za su gudu. Abin da ya sa ke nan Joshua ya yi wa Jehobah addu’a kuma ya ce: ‘Rana, tsaya wuri ɗaya!’ Da rana ta ci gaba da haskakawa, Isra’ilawan suka kammala cin nasara a yaƙin.

Da akwai miyagun sarakuna da yawa a ƙasar Kan’ana da ba sa son mutanen Allah. Ya ɗauki Joshua da sojojinsa wajen shekara shida kafin su kammala cin sarakuna 31 a yaƙi. Bayan da suka gama wannan, Joshua ya tabbata an raba waɗannan ƙasa ga ƙabilu da har yanzu suna bukatar yanki.

Shekaru da yawa suka shige, Joshua ya mutu a ƙarshe yana da shekara 110. Sa’ad da shi da abokansa suke da rai, mutane suna yi wa Jehobah biyayya. Amma sa’ad da waɗannan mutanen kirki suka mutu, mutanen suka fara yin miyagun abubuwa kuma suna shiga cikin masifa. Wannan lokaci ne da suke bukatar taimakon Allah sosai.

Joshua 10:6-15; 12:7-24; 14:1-5; Alƙalawa 2:8-13.