Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 50

Mata Biyu Marasa Tsoro

Mata Biyu Marasa Tsoro

SA’AD da Isra’ilawa suka shiga masifa, sun yi wa Jehobah kuka. Jehobah ya amsa musu ta wajen ba su shugabannai marasa tsoro. Littafi Mai Tsarki ya kira waɗannan shugabannai alƙalai. Joshua ne alƙali na fari, wasu alƙalai kuma na bayansa sune Othniel, Ehud da Shamgar. Biyu daga cikin mutanen da suka taimaki Isra’ila mata ne masu suna Deborah da Jael.

Deborah annabiya ce. Jehobah yana ba ta bayani game da abin da zai faru a nan gaba, sai kuma ta gaya wa mutanen abin da Jehobah ya ce. Deborah kuma alƙali ce. Tana zaune a ƙarƙashin wani dabino a can wuri mai tuddai, kuma mutane suna zuwa wurinta domin taimako.

A wannan lokaci Jabin ne sarkin Kan’ana. Yana da karusai 900. Rundunarsa tana da ƙarfi sosai da har aka tilasta wa Isra’ilawa da yawa suka zama bayin Jabin. Sunan shugaban sojojin Jabin shi ne Sisera.

Wata rana Deborah ta aika wa Alƙali Barak saƙo ta ce masa: ‘Jehobah ya ce: “Ka ɗauki mutane 10,000 ka ja-gorance su zuwa Dutsen Tabor. A nan zan kawo maka Sisera. Zan ba ka nasara bisansa da kuma sojojinsa.”’

Barak ya ce wa Deborah: ‘Zan je idan ke ma za ki tare da ni.’ Deborah ta bi shi, amma ta ce wa Barak: ‘Ba za ka sami yabo ba domin nasarar, domin Jehobah zai ba da Sisera ga hannun mace.’ Kuma abin da ya faru ke nan.

Barak ya hau daga Dutsen Tabor domin ya haɗu da sojojin Sisera. Farat ɗaya Jehobah ya tura ambaliya kuma yawancin sojojin abokan gaba suka mutu. Amma Sisera ya sauka daga kan karusarsa ya gudu.

Bayan wani ɗan lokaci Sisera ya isa tantin Jael. Ta gayyace shi cikin tantin, ta ba shi madara ya sha. Wannan ya sa ya fara jin barci, ba da daɗewa ba ya fara sheƙa barci. Sai Jael ta ɗauki ƙusa na tanti ta buga shi a kan wannan mugun mutum. Daga baya, sa’ad da Barak ya isa, ta nuna masa gawar Sisera! Ka ga abin da Deborah ta faɗa ya zama gaskiya.

A ƙarshe aka kashe Sarki Jabin ma, Isra’ilawa suka sami kwanciyar hankali na ɗan lokaci.

Alƙalawa 2:14-22; 4:1-24; 5:1-31.