Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 53

Alkawarin Jephthah

Alkawarin Jephthah

KA TAƁA yin alkawari kuma daga baya ya yi maka wuya ka cika? Wannan mutumin na hoton nan ya yi haka, kuma abin da ya sa ke nan yake baƙin ciki. Mutumin gwarzon alƙali ne na Isra’ila mai suna Jephthah.

Jephthah ya rayu ne a lokacin da Isra’ilawa ba sa bauta wa Jehobah. Suka sake komawa ga yin miyagun abubuwa. Saboda haka Jehobah ya ƙyale mutanen Ammon su zalunce su. Hakan ya sa Isra’ila suka yi kuka ga Jehobah: ‘Mun yi maka zunubi. Don Allah, ka cece mu!’

Mutanen suka tuba daga miyagun abubuwa da suke yi. Suka nuna cewa sun tuba ta wajen komawa ga bautar Jehobah. Sai Jehobah ya sake taimakonsu.

Mutanen suka zaɓi Jephthah ya yaƙi Ammonawa. Jephthah yana so Jehobah ya taimake shi a yaƙin. Saboda haka ya yi wa Jehobah alkawari: ‘Idan ka ba ni nasara bisa Ammoniyawa, mutumin da ya fito daga gidana da farko ya tare ni sa’ad da na yi nasara zan ba ka shi.’

Jehobah ya saurari alkawarin Jephthah, kuma ya taimake shi ya ci nasara. Sa’ad da Jephthah ya koma gida, ka san waye ya fara zuwa taransa? ’Yarsa ce, tilonsa. ‘Wayyo, ’ya ta!’ in ji Jephthah. ‘Kin jawo mini baƙin ciki. Amma na yi wa Jehobah alkawari, kuma ba zan fasa cika shi ba.’

Sa’ad da ’yar ta fahimci alkawarin da ya yi, da farko ta yi baƙin ciki ƙwarai. Domin wannan yana nufin dole ne ta bar babanta da ƙawayenta. Ta ƙarasa sauran rayuwarta a mazaunin Jehobah a Shiloh. Saboda haka ta gaya wa babanta: ‘Idan ka yi wa Jehobah alkawari, to dole ka cika.’

Saboda haka ’yar Jephthah ta je Shiloh, ta ƙarasa sauran rayuwarta tana bauta wa Jehobah a mazauni. Kwanaki huɗu a kowane shekara ’ya’ya mata na Isra’ila suna zuwa su ziyarce ta a can, suna yin farin ciki tare. Mutanen suka ƙaunaci ’yar Jephthah sosai domin baiwar kirki ce ta Jehobah.

Alƙalawa 10:6-18; 11:1-40.